Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon CJN Tanko Muhammad

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon CJN Tanko Muhammad

  • Tsohon shugaban alkalan Najeriya, Tanko Muhammad ya yi murabusa daga matsayin a ranar Litinin, 27 ga watan Yunin 2022
  • Tanko wanda ya kasance dan asalin jihar Bauchi ya ajiye mukamin nasa ne bisa dalili na rashin lafiya
  • Kafin ya zama shugaban alkalan kasar ya rike mukamai daban-daban ciki harda alkalin kotun daukaka kara da kuma Khadi na kotun shari’a ta yankin Bauchi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A safiyar ranar Litinin, 27 ga watan Yuni ne aka wayi gari da labarin murabus din shugaban alkalan Najeriya kuma shugaban majalisar shari’a ta kasa, CJN Ibrahim Muhammad Tanko.

Hadimin tsohon shugaban alkalan kasar, Yusuf Isah, ya kuma tabbatar da batun inda ya bayyana dalili na rashin lafiya a matsayin hujjar ubangidan nasa na sauka daga mukamin nasa.

Tanko Muhammad
Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon CJN Tanko Muhammad Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Legit.ng ta yi amfani da wannan kafar domin jero wasu muhimman abubuwa da ya kamata a sani game da tsohon shugaban alkalan na Najeriya.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa da ya Kamata a Sani Game da Sabon CJN Olukayode

  1. Justis Tanko Muhammad Bafilatani ne, an kuma haife shi ne a ranar 31 ga watan Disamban 1953.
  2. Ya fito daga yankin Doguwa a karamar hukumar Giade ta jihar Bauchi.
  3. Ya yi karatunsa na firamare a makarantar Giade daga 1961 zuwa 1968 sannan ya tafi makarantar sakandare ta gwamnati da ke Azare a 1969 inda ya mallaki takardar shaidar WAEC a 1973.
  4. Daga nan Tanko ya tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya mallaki digiri a bangaren shari’ar Musulunci daga 1976 zuwa 1980.
  5. Ya kuma mallaki digiri na biyu da na uku a bangaren shari’a daga jami’ar ABU a 1985 da 1998.
  6. An rantsar da Tanko a matsayin lauya a 1981, shekarar da ya kammala daga makarantar shari’a ta Najeriya, sannan ya fara aiki a 1982.
  7. Tanko ya rike manyan mukamai daban-daban ciki harda alkalin kotun shari’ar musulunci na yankin Bauchi da kuma alkalin kotun daukaka kara.
  8. An nada shi a matsayin alkali a kotun koli na Najeriya a 2006 amma sai a ranar 7 ga watan Janairu 2007 aka rantsar da shi.
  9. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Tanko a ranar 11 ga watan Yulin 2019, a matsayin shugaban alkalan Najariya kuma shugaban majalisar shari’a ta kasasannan aka rantsar da shi a ranar 24 ga watan Yulin 2019,
  10. Tanko Muhammad ya yi murabusa daga matsayin shugaban alkalan Najeriya a ranar Litinin, 27 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Rashawa? Dalilai masu karfi guda 5 da suka sa shugaban alkalai ya ajiye aikinsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hotuna: Jastis Olukayode Ya Karba Rantsuwar Kama Aiki Matsayin Mukaddashin CJN

A wani labarin, mun ji cewa Justis Olukayode Ariwoola na kotun koli ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Najeriya a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya rantsar da Justis Ariwoola a yayin wani biki da aka gudanar a zauren majalisa na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng