Hotuna da Bidiyon Kyakyawar Budurwa da Tace Zata Baiwa Ɗiyar Ekweremadu Kyautar Ƙoda
- Martha Uche ta ce a shirye ta ke da ta sadaukar da kodarta don ceto rayuwar 'diyar Sanata Ike Ekwdremadu
- Matashiyar budurwar da ke zaune a Illorin ta ce ta hango hakan a mafarki kuma a yanzu ta shirya yin hakan ba tare da ta bukaci komai daga wani ba
- Idan za a tuna, 'yan sanda birnin London suna tuhumar Ekwdremadu da matarsa, Beatrice, da laifin safarar wani yaro zuwa UK don cire masa koda
Kwara - Wata matashiya 'yar Illorin mai suna Martha Uche ta bayyana yadda ta shirya sadaukar da kodarta don ceto rayuwar 'diyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekwdremadu.
Idan za a tuna, 'yan sanda birnin London suna zargin Ekweremadu da matarsa Beatrice da laifin safarar wani yaro zuwa Amurka don cire sassan jikinsa, kamar yadda hukumar shari'ar ta bayyana a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Miss Martha Uche ta ce a shirye ta ke da ta sadaukar da kodarta don ceto rayuwar 'diyar Ike Ekwdremadu.
An ki bada belin tsohon 'dan majalisar da matarsa bayan 'yan sandan birnin London sun gurfanar dasu gaban kotun majistare ta Uxbridge a London.
Matashiyar, wacce ta zanta da Legit.ng ta ce a shirye ta ke da ta taimaki 'diyar Ekweremadu.
A cewarta: "Ina so in taimake ta hanyar sadaukar da daya daga cikin kodojina gareta. Ina son taimaka mata saboda na riga na ganta, sannan an nunamin a mafarki na."
Yayin martani ga masu ganin za ta sadaukar da kodarta kyauta ko kuma don a bata 'yan canji. Ta kara da cewa: "Kawai ina so in taimaki yarinyar ne saboda tana matukar bukatar taimako. Duk abun da suke da shi za su iya badawa, amma a yanzu damuwata shi ne lafiyar yarinyar."
Yayin da aka tambayeta a kan abun da ka iya biyo bayan matakin da zata dauka, ta ce: "Babu abun da zai same ni. An riga an kaddara. Ina da cikakkiyar lafiya, ina dadewa ban yi ciwo ba. Tun ina karama, ina dadewa ban yi ciwo ba."
Yayin da aka tambayeta ko ta shirya taimakon wasu, cewa tayi kawai ita burinta shi ne ta taimaki 'diyar tsohon shugaban majalisar dattawa.
Ta kara da cewa: "Ita kadai nake son taimakamawa."
Asali: Legit.ng