Hukuncin kotun koli kan Hijabi: Yanzu karyarku ta kare, wajibi jihohin Yarabawa suyi biyayya: MURIC

Hukuncin kotun koli kan Hijabi: Yanzu karyarku ta kare, wajibi jihohin Yarabawa suyi biyayya: MURIC

  • MURIC ta yi tsokaci kan hukuncin kotun koli da tayi watsi da dokar hana sanya Hijabi a makarantun Legas
  • Kungiyar MURIC ta yi kira da dukkan sauran jihohin kudu maso yamma suyi biyayya yanzu saboda karyarsu ta kara
  • Kotun kolin Najeriya ta kawo karshen dambarwan bayan shekaru takwas ana kai ruwa rana

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Kungiyar kare hakkin Musulmai watau Muslim Rights Concern (MURIC), ta yi murnar hukuncin kotun koli wacce ta halastawa dalibai mata sanya Hijabinsu a jihar Legas.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar a shafin kungiyar na yanar gizo.

Yace:

"Gaskiya ta murkushe karya. Komin dadewa, gaskiya za tayi galaba kan karya. Muna jinjinawa Alkalan da suka tabbatar da gaskiya."
"Wannan ya zama izina ga makiya addinin Musulunci masu kokarin cirewa 'yaya mata Hijabansu a fili.

Kara karanta wannan

Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

"Tunda kotun koli itace kotun Allah ya isa. Muna kira ga dukkan makarantun gwamnati da shugabannin makarantu a Kwara, Oyo, Osun, Ogun, Ondo, Ekiti, Edo, su yi biyayya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC
Hukuncin kotun koli kan Hijabi: Yanzu karyarku ta kare, wajibi jihohin Yarabawa suyi biyayya: MURIC Hoto: Imedia
Asali: Facebook

Musulmai sun yi nasara, kotun koli tayi watsi da dokar hana sanya Hijabi a makarantun Legas

Kotun koli ta baiwa Musulmai gaskiya inda tayi watsi da karar da gwamnatin jihar ta shigar kan hana dalibai mata Musulmai sanya Hijabi a makaratun dake fadin jihar.

A hukuncin da kotun ta yanke ranar Juma'a, 17 ga watan Yuni, 2022, ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara tayi ranar 21 ga Yuli, 2016.

Cikin alkalan kotun koli bakwai da suka zauna kan lamarin, biyar sun amince a bari daliban su sanya Hijabansu yayinda biyu suka ce basu yarda ba, rahoton TheNation.

Alkali Kudirat Kekere-Ekun, wacce ta rubuta shari'ar da Alkali Tijjani Abubakar, ya karanto ranar Juma'a, tace ayi watsi da karar gwamnatin Legas saboda babu gaskiya ciki.

Kara karanta wannan

An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: