Dalilin da yasa nike son zama mataimakin Tinubu, Simon Lalong
- Gwamna Simon Lalong na Plateau ya bayyana cewa yana son zama mataimakin shugaban kasa na Tinubu a zabe
- Simon Lalong shine shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya kuma mabiyin addinin Kirista
- Lalong na cikin wadanda ake kyautata zaton Asiwaju Bola Tinubu da jam'iyyar APC zasu zaba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalnong, ya nuna niyyar son zama abokin tafiyar dan takarar shugaban kasar APC, Aiwaju Bola Tinubu, saboda ya cancanta, ba don addininsa ba.
Lalong ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da gidan talabijin Trust TV.
An ruwaitosa da cewa,
"Ba wai ina son zama mataimakin shugaban kasa don addini na bane; ina son zama ne don na cancanta."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kamata a dama da kowa, Lalong
Lalong ya bayyana cewa ya kamata a dama da kowa saboda idan akayi watsi da tsohon tsarin Musulmi-Kirista da ake amfani, wannan na iya zama matsala.
Yayinda aka tambayesa shin ta wace hanya ya magance matsalar rikice-rikicen addinin a jihar Plateau, Lalong yace:
"Na fahimci cewa wasu rikice-rikicen na faruwa a Plateau ne saboda mayar da wasu saniyar ware. Wasu na ganin an yi watsi da su."
"A siyasa, akan ce masu rinjaye na samun abinda suke so amma a baiwa marasa rinjaye daman fadin ra'ayoyinsu. Idan kayi hakan, zaka samu zaman lafiya."
Asali: Legit.ng