Dan Dora Akunyili: Fastoci Sun Rika Tatsar Kudin Mahaifiyana Da Sunan Za Su Yi Mata Maganin Cutar Kansa
- Dan marigayiya Mrs Dora Akunyili, Obumnaeme ya bayyana yadda wasu fastoci suka rika tatsar kudin mahaifiyarsa da suna yi mata maganin kansa
- Ya bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a baya-bayan nan yana mai cewa abin da suka yi mata damfara ne da ci da addini duk da ba kallon da ake masa kenan ba a Najeriya
- Farfesa Dora Akunyili ta rike mukamin shugaban hukumar NAFDAC da kuma ministan watsa labarai, daga baya ta rasu bayan ta yi jinyar cutar kansa
Obumnaeme, dan marigayiya Mrs Dora Akunyili, tsohuwar Ministan Sadarwa, ya bayyana yadda wasu fastoci suka rika karbar kudin hannun mahaifiyarsa da sunan za su warkar da ita daga ciwon daji wato kansa.
Ya bayyana hakan ne yayin hira da Chude Jideonwo, Direkta Janar na Ofishin Kula da Kwangiloli da Ayyuka na Jihar Anambra, kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, mahaifiyarsa ta tafi wuraren wasu fitattun fastocin Najeriya a yunkurinta na neman waraka bayan an gano tana da kansa wanda ya kai mataki na 4.
Ya ce wasu da yawa daga cikinsu sun yi amfani da damar suka rika karbar kudi daga hannunta duk da sun san cewa ba za su iya mata maganin ba, ya kara da cewa abin da fastocin suka yi wa mahaifyarsa 'ci da addini ne'.
Obumnaeme ya ce:
"Ta kan ce Ubangiji zai warkar da ni; Ta kashe dukkan kudin, ta bada sadaka. Ina ganin tamkar damfara ne. A Najeriya, ba mu kiransa laifi amma ina ganin damfara ne.
"Ta tafi wurin wani fasto a Legas tsawon mako guda. Ta dawo ta a tafi a yi skanin domin Ubangiji ya warkar da ita. Na tuna mahaifi na yana kuka a lokacin da zai kai ta wurin hoton skanin din. Ya san abin da za a gani. Amma baya son zuciyarta ta karaya, baya son yanke mata tsammani.
"Amma mahaifiyata, cewa ta ke 'Allah ya warkar da ni'. Suka tafi suka gano cewa kansar na nan, ta kara girma, sai mahaifiyata ta zama tamkar kwankwo tsawon kwana uku. Kana kallon mutumin da ke cike da rayuwa yana zagwanyewa a kullum."
An Rage Wa Wasu Farfesoshi Uku Mukami a Jami'ar Adamawa
A wani rahoton, Jami'ar Modibbo Adama ta Jihar Adamawa, MAU, ta rage wa wasu farfesoshi uku mukami saboda samunsu da laifuka masu alaka da karatu, Daily Trust ta rahoto.
Mataimakin shugaban jami'ar, bangaren mulki, Farfesa Muhammad Ja'afaru, ne ya sanar da hakan a bikin cika shekara uku na Farfesa Abdullahi Tukur, Shugaban MAU, a ranar Asabar a Yola.
Ya ce an mika batun ga sashin hukunta masu laifi a jami'ar kuma aka amince da rage wa malaman da abin ya shafa mukami.
Asali: Legit.ng