Dan shekara biyu ya bindige mahaifinsa har lahira yayin wasa da bindiga a Amurka
- Karamin yaro dan shekara biyu ya kashe mahaifinsa a birnin Florida ta kasar Amurka da bindiga
- Yayinda aka kai mahaifin asibiti don farfado da shi, likitoci suka sanar da cewa ya mutu sakamakon harbin
- Gwamnatin Amurka ta halastawa daidaikun mutane saya da rike bindiga don kare kawunansu
Wani yaro dan shekara biyu ya harbe mahaifinsa har lahira a Amurka yayin wasa da bindigar da iyayensa suka ajiye, hukumomi a birnin Florida ta Amurka suka bayyana ranar Litnin.
Yayinda jami'an yan sanda suka dira gidan ranar 26 ga Mayu, sun ga mahaifiyar yaron, Marie Ayala, na kokarin farfado da mijinta, Reggie Mabry, rahoton AFP.
Da farko jami'an tsaro sun dauka mahaifin ne ya harbe kansa amma daya daga cikin yaran gidan ya bayyanawa mahukunta cewa kaninsu dan shekara biyu ne yayi harbin, Shugaban hukumar yan sandan yankin John Mina ya bayyana haka a hira da manema labarai.
Yace:
"Masu bindiga basu ajiye makamansu da kyau kuma dan sakacin lokaci kadan sai kaji wani mumunan abu ya faru."
"Yanzu wadannan yaran sun rasa iyayensu duka. Mahaifin ya mutu. Mahaifiyarsu na kurkuku."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ire-iren wadannan abubuwa na faruwa a Amurka.
A Agustan 2021, wani dan shekara biyu haka ya bindige mahaifiyarsa yayinda take waya.
Asali: Legit.ng