Yanzun nan: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya daga Madrid

Yanzun nan: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya daga Madrid

  • Shugaban kasar Najeriya ya kammala ziyarar da ya kai kasar Andalus kuma ya dawo Najeriya
  • Buhari ya kwashe kwanaki uku a Andalus yana ganawa da mutane daban-daban ciki har da yan kasuwa
  • Fadar shugaban kasa tace Buhari ne shugaban Najeriya na farko da ya taba zuwa Andalus ziyara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Madrid - Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga babbar birnin kasar Andalus, Madrid, kuma ya dira Abuja bayan ziyarar kwana uku da ya kai.

Shugaban ya tashi daga Torrejon Airbase, Madrid, misalin karfe 8 na safiyar Juma'a, kuma ya dira bayan Sallar Juma'a, hadiminsa, Buhari Sallau ya bayyana.

A kwanaki uku da yayi a Madrid, Buhari ya gana da Shugaban kasar Andalus, Pedro Sanchez da kuma Sarkin kasar King Felipe VI.

Yayin ganawarsa da Shugaba Sanchez; Najeriya da Andalus sun rattafa hannu kan yarjejeniya tara wanda ya hada da yarjejeniyar mikawa juna mai laifi, matsalar rashin tsaro, harkokin al'adu da Kimiya da fasaha.

Kara karanta wannan

Buhari ya taso daga Madrid, yana hanyarsa ta dawowa Najeriya

Hakazalika ranar Alhamis, ya halarci taron yan kasuwa da yan siyasa da cibiyar kasuwancin Andalus ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzun nan: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya daga Madrid
Yanzun nan: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya daga Madrid Hoto: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

Bayan haka ya gana da yan Najeriya mazauna Andalus, wanda ya hada da yan kwallo da wasu masu zuba jari dake da niyyar zuwa Najeriya.

Buhari ya samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Antoni Janar, Abubakar Malami (SAN); Ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Adeniyi Adebayo; Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed da Ministan harkokin cikin gida, Rauf AregbeSola.

Sauran sun hada da Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare; mataimakin Ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora; NSA Babagana Munguno; Shugaban hukumar leken asiri, Amb Ahmed Rufa'i Abubakar da shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng