Bidiyo: Mata da mijin da basu da cin yau balle na gobe sun haifa 'yan 4 reras, suna neman taimako

Bidiyo: Mata da mijin da basu da cin yau balle na gobe sun haifa 'yan 4 reras, suna neman taimako

  • Wasu ma'aurata dake rayuwa a Anyaa a yankin Accra sun haifa 'yan hudu da suka hada da maza 2, mata 2
  • Abena Serwaa, tana sana'ar gyaran gashin kan mata yayin da mijinta Kwesi Addie yake gyaran wuta kuma basu da takamaiman wurin samun kudi
  • Ma'auratan suna kira ga jama'a masu wadata da su taimaka musu a yayin da suka zama iyayen 'ya'ya hudu a lokaci daya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ghana - Wasu ma'aurata 'yan asalin kasar Ghana masu suna Abena Serwaa da Kwesi Addie da ke rayuwa a Anyaa a yan kin Accra sun haifa 'yan hudu reras, biyu mata, biyu maza.

Ma'auratan suna da yara mata biyu, hakan ne yasa suka kai au takwas har da matar da mijin.

Bidiyo: Mata da mijin da basu da cin yau balle na gobe sun haifa 'yan 4 reras, suna neman taimako
Bidiyo: Mata da mijin da basu da cin yau balle na gobe sun haifa 'yan 4 reras, suna neman taimako. Hoto daga Crime Check TV GH
Asali: UGC

A wata tattaunawa da suka yi yi Crime Check TV GH, mahaifiyar 'yan hudun ta bayyana cewa likitoci tun farko sun bayyana mata cewa 'yan uku za su haifa.

Kara karanta wannan

Cakwakiya: Wata mata ta ba da labarin yadda ta auri yayanta har suka haifi 'ya'ya 4

Abena Serwaa ta gano cewa 'ya'ya hudu ne a cikinta yayin da ta je haihuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar da mijinta sun matukar girgiza tare da bayyana tsoronsu a lokacin da likitoci suka sanar musu yawan jinjiran da ke cikinta inda suka ce sun san ba za su iya kula da su ba.

A halin yanzu, suna rayuwa ne a saki daya da ke Anyaa tare da 'ya'yansu shi da reras.

Duk mai son taimakawa wadannan iyalan zai iya kiran lambar waya kamar haka: 0242074276

Ga bidiyonsu a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: