Kashe Deborah: Ƙungiyoyin Musulmai 13 sun shawarci gwamnatin Buhari kan zagin Annabi da ɗaukar doka a hannu

Kashe Deborah: Ƙungiyoyin Musulmai 13 sun shawarci gwamnatin Buhari kan zagin Annabi da ɗaukar doka a hannu

  • Kungiyoyin Musulmai 13 sun yi kira ga gwamnati ta yi wa waɗan da aka kama da kashe Deborah Samuel adalci
  • Kungiyoyin ƙarƙashin inuwar MURIC mai fafutukar kare haƙƙin musulmai a Najeriya sun shawarci gwamnati kan hanyar kawo karshen irin haka
  • Sun kuma yi kira ga Malaman addinin kirista kan su kula da ɗora mabiyan su kan tafarkin girmama addinai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kungiyoyin Addinin Musulunci 13 ƙarƙashin inuwar kungiyar Musulmai masu rajin zaman lafiya da adalci ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi wa mutanen da suka kashe Deborah Samuel adalci.

Daily Trust ta rahoto cewa Deborah, ɗaliba a kwalejin horar da malamai ta tunawa da Shehu Shagari da ke Sokoto, ta mutu ne bayan ta zagi Annabi SAW, matasa suka zuciya.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

Kungiyoyin sun kuma roki FG ta karfafa ko kuma ta kikriri doka ta musamman kan masu ɓatanci da kuma masu ɗaukar ɗoka a hannu idan an yi ɓatanci, kuma ta tilasta bin dokokin.

Deborah Samuel.
Kashe Deborah: Ƙungiyoyin Musulmai 13 sun shawarci gwamnatin Buhari kan zagin Annabi da ɗaukar doka a hannu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Farfesa Lakin Akintola, mai fafutukar kare haƙƙin Musulmai kuma daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) shi ya faɗi haka a wurin taron manema labarai a Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tare da wasu shugabannin Musulunci, Akintola ya nemi a yi wa mutanen Adalci, "Ba tare da diba munin abinda suka aikata ko kuma abin da suka yi ikirarin ya ja su."

Ya ce za'a iya amfani da irin wannan abun mai muni wajen daƙile yaɗuwar zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci, inda ya ƙara da cewa:

"Waɗan nan abu ne da zamu cimma cikin sauki matuƙar kowane mabiyin Addini zai rungumi koyarwar addininsa ya kuma yi aiki da sakon cikin imani."

Kara karanta wannan

Bayan Kashe wacce ta zagi Annabi, Yan sanda sun gana da Malamai da masu ruwa da tsaki

Tilas mu girmama addinan juna

Ya kuma yi kira ga shugabannin Kiristoci su sa ido tare da amfani da duk wata damar su wajen jawo hankali kiristoci su rinka girmama Addinin Sauran mutane.

Akintola ya ce:

"Muna tare da muryoyin Malaman Musulunci kuma a shirye muke mu yi aiki tare don inganta ginshikin zaman lafiyan ƙasar mu, sasanci da kuma fahimtar juna."
"Muna rokon Malaman Addinai su zage dantse wajen wayar da kan mabiyansu girman mahimmancin girmama sauran addinai, maida hakali wajen nuna kauna da kauce wa kiyayya da tsattsauran ra'ayi."

A wani labarin kuma Matasan Musulmai sun fito neman matar da ta zagi Annabi ruwa a jallo a Bauchi, an harbe mutum 2

Fusatattun matasa a jihar Bauchi sun bazama neman matar da ta taba mutuncin Annabi Muhammad.

Sai dai matasan sun farma wasu kiristoci tare da lalata kayayyaki mallakarsu sakamakon rashin ganin matar wacce tuni aka boye ta.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban ƙasa a APC da suka sayi Fom N100m kuma suka gaza maida wa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262