Matasa sun fi karfin jami'an DSS da sukayi kokarin ceton Deborah, Tambuwal
- Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto yace daya daga cikin jami'an DSS da yayi kokarin ceton rayuwarta yana kwance a asibiti
- Tambuwal ya kara da cewa matasan da karfi suka kwace Deborah hannun jami'an tsaro
- A cewarsa, an fasa wa jami'an DSS kai kuma an karya masa kafa yayinda yake kokarin ceton Deborah
Delta - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a ranar Juma'a ya yi karin haske kan abinda ya auku tsakanin jami'an tsaro da matasan Sokoto kan dalibar da tayi batanci ga Manzon Allah, Deborah.
Tambuwal ya bayyana cewa sabanin tunanin da mutane ke yi, jami'an hukumar DSS sun yi kokarin cetonta amma daliban makarantan sun fisu yawa kuma suka fi karfinsu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya ziyarci jihar Delta a yakin neman zaben da yake yi, rahoton ChannelsTV.
Yace:
"Sabanin abinda kuke tunani, jami'an tsaro musamman DSS sun samu shiga makarantar da wuri kuma sukayi kokarin ceton Deborah daga wajen matasan."
"Yayinda ake kiran Sojoji da yan sanda, matasan na kara yawa. Yanzu haka daya daga cikin jami'an DSS da yayi kokarin ceton rayuwarta yana kwance a asibiti an fasa masa kai kuma an karya masa hannu."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba barinta muka yi kara zube ba, an fi karfinsu ne."
Gwamnan ya yi watsi da kalaman cewa jami'an tsaro basu yi komai wajen cetota ba.
Zagin Annabi: Soyinka Ya Ce Dole a Sauke Maqari Daga Limanci a Abuja Soboda Ya Goyi Bayan Kashe Deborah
Fitaccen marubuci wanda ya taba lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira da a sauke limamin babban masallacin kasa na Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, daga mukaminsa kan kalaman da ya furta game da kisar Deborah Yakubu, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto saboda zagin Annabi (SAW).
The Punch ta rahoto cewa Soyinka ya zargi limamin da umurtar mabiyansa su dauki doka a hannunsu da sunan addini.
Ya yi wannan jawabin ne a ranar Asabar a Abuja yayin taron shekara guda da rasuwar tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da kaddamar da littafin tarihinsa da marubuci Niran Adedokun ya rubuta.
Asali: Legit.ng