Bayan Kwana Uku a Tsare, EFCC Ta Sako Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Bayan Kwana Uku a Tsare, EFCC Ta Sako Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Abuja - Hukumar Yaki da Rashawa da yi wa arzikin kasa ta'anatti, EFCC, ta sako tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Mrs Patricia Etteh, wacce aka kama kan zargin damfara.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mai magana da yawun EFCC, Mr Wilson Uwujaren, ya bayyana sakin ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, rahoton Channels Television.

EFCC Ta Sako Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya
Hukumar EFCC Ta Sako Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Patricia Etteh. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

An saki Mr Etteh ne a ranar Juma'a, kwana uku bayan kama ta,"bayan cika ka'idojin beli da wadanda ke bincike a kanta suka bada," a cewar sanarwar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Za ta rika zuwa ofishin na EFCC lokaci zuwa lokaci domin cigaba da amsa tambayoyi," EFCC ta kara da cewa.

An kama tsohuwar Kakakin Majalisar ne kuma hukumar ta tsare ta a ranar Talata kan zarginta da karbar wasu kudade da ake zargin ba tsaftattu bane cikin kudin kwangilar da aka bawa Phil Jin Projects.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya nada Dr Tutuwa Adamu matsayin shugabar FIIRO

An zabe ta Kakakin Majalisa ne a shekarar 2007 amma ta yi murabus bayan watanni kadan kan zarginta da bannatar da kudade.

Ita ce mace ta farko kuma tilo da ta taba rike mukamin Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya a tarihin Najeriya.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164