Shugaba Buhari ya nada Dr Tutuwa Adamu matsayin shugabar FIIRO

Shugaba Buhari ya nada Dr Tutuwa Adamu matsayin shugabar FIIRO

  • Shugaba Buhari ya nada sabuwar shugabar hukumar bincike na fasaha ta Najeriya
  • Hukumar ta FIIRO na karkashin ma'aikatar Kimiya da Fasaha, wacce ba tada Minista yanzu tun bayan murabus din Ogbonnya Onu
  • Shugaban kasan yanzu haka ya tafi hadaddiyar daular larabawa don kai gaisuwar ta'aziyya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Dr. Adamu Tutuwa matsayin Dirakta Janar na hukumar binciken masana'antun tarayya watau Federal Institute of Industrial Research, Oshodi FIIRO.

Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar Kimiya da Fasaha, Mrs. Monilola Udoh, ce ta fitar da sanarwar ranar Juma'a a jihar Legas, rahoton Tvcnewsng.

Shugaba Buhari ya nada Dr Tutuwa Adamu matsayin shugabar FIIRO
Shugaba Buhari ya nada Dr Tutuwa Adamu matsayin shugabar FIIRO Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

A cewar sanarwar, Dr Adamu Tutuwa ta kasance Diraktar hukumar hukumar cigabar fasahar ilmin hallita na tarayya watau National Biotechnology Development Agency, shiyyar Jalingo, jihar Taraba gabanin sabon nadin da aka yi mata.

Kara karanta wannan

Bayan Kwana Uku a Tsare, EFCC Ta Sako Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta kara da cewa Dr Tutuwa na da kwarewa wajen bincike da cigaban kimiya kuma hakan zai taimaka wajen bincike don samar da abubuwan cigaba ga kasa.

A cewarta:

"Muna kyautata zaton zata amfanar da hukumar bisa kwarewarta a fasahar ilmin halitta da alakarta da kungiyoyi masu bada gudunmuwa."

Za ta rike wannan kujera na tsawon shekaru biyar, fari daga ranar 10 ga Mayu, 2022.

Buhari ya nada mai taimaka masa kan samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Misis Matilda Mmegwa a matsayin babbar mai ba shugaban kasa shawara kan dauka da samar da aikin yi.

Sabuwar hadimar shugaban kasar wacce ta rike mukamai daban-daban a kamfanoni masu zaman kansu a Kanada da kungiyoyin kasa da kasa, za ta yi aiki ne a karkashin shugabancin ministan kwadago da daukar ma’aikata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai, Mista Femi Adesina, ya saki a ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: