Adadin mutanen da ake kashe da wadanda akayi garkuwa dasu a Kaduna cikin watanni 3
- Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana adadin mutanen da yan bindiga suka sace cikin watanni uku a jihar
- Yan bindiga sun addabi al'ummar jihar Kaduna musamman baban titin Abuja zuwa Kaduna
- Gwamnan jihar Kaduna ya bada shawaran tayar da garin Rijana, Katari da Akilubu gaba daya
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana damuwarsa bisa yawaitan yan ta'adan Ansaru da na Boko Haram a jihar Kaduna.
Gwamnan ya bayyana cewa hakazalika akwai sabon alaka dake gudana yanzu tsakanin yan bindiga masu garkuwa da mutane da yan Boko Haram.
A cewarsa, wannan alaka ta haifar da harin da aka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga Maris, 2022.
Ya bayyana haka ne a zaman majalisar tsaron jihar na watanni uku-uku da kwamishanan tsaron jihar, Samuel Aruwan, ke gabatar da bayanan tsaro, rahoton TVCng
Malam El-Rufa'i a jawabinsa ya kara da cewa yanzu yan ta'adda sun fara dasa bama-bamai a jihar.
Saboda haka yana kira ga gwamnatin tarayya ta kafa tiyata na Sojoji a jihar kamar yadda aka yi a Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shi kuma Kwamishanan tsaron, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa akalla mutum 360 aka kashe sakamakon hare-haren yan bindiga kuma an yi garkuwa da mutane 1,389 tsakanin watar Junairu da Maris na shekarar nan.
A cewarsa, mazabar tsakiyar Kaduna wannan kashe-kashe da hare-hare suka fi aukuwa.
Yan bindiga sun sako matar da ta shiga daji taimakawa Fulani, sun rike diyarta da direba
Malama a kwalejin fasahar KadPoly wacce yan bindiga suka sace lokacin da ta shiga daji rabawa Fulani kayan azumi, Dr Rahmatu Abarshi, ta samu kubuta.
A watan Afrilu, yan bindiga sun saceta tare da diyarta da direbanta.
Shugaban kamfanin Liberty TV da safiyar Alhamis ya tabbatar da labarin cewa an sako ta.
A cewarsa:
"An sak Lakcarar amma diyarta, Ameerah da direbanta har yanzu na hannun yan bindigan"
Asali: Legit.ng