'Yan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

'Yan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

  • Dan tsohon Sifeta Janar na ‘Yan Sanda ya bayyana ra’ayinsa dangane da kisan Miss Deborah Samuel Yakubu da ‘yan makarantarsu su ka yi a Sokoto
  • Kamar yadda Captain Jamil Abubakar ya shaida, yawancin addinai, har da addinin kirista, sun tanadar da kisa ya zama hukuncin duk wanda ya yi batanci ga addini
  • Hakan ya sa ya hori duk wani dan Najeriya da ya kasance mai girmama addinin dan uwansa don a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali

Captain Jamil Abubakar, dan tsohon Sifeta Janar na ‘Yan sanda, Mohammed Abubakar ya nuna amincewarsa dangane da kisan wacce ta yi batanci a Sokoto, The Punch ta ruwaito.

Jamil, wanda matukin jirgin sama ne kuma shugaban cibiyar JMD, a wata wallafarsa ta Twitter a ranar 13 ga watan Mayu ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

'Dan Tsohon IGP Ya Goyi Bayan Kashe Ɗalibar Da Ta Zagi Annabi a Sokoto, Ƴan Najeriya Sun Yi Martani
'Dan Tsohon IGP Ya Ce Kisa Ne Hukuncin Batanci. Photo credit: Kennytee Obaomo.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Deborah, dalibar kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, ita ce wacce dalibai musulmai su ka halaka ta tare da babbake gawarta a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu bisa zarginta da yin batanci ga manzon Allah Muhammad SAW.

Jamil, wanda siriki ne ga mai kudin duniya, Aliko Dangote, ya bayyana wannan ra’ayin nasa ana tsaka da cece-kuce akan kisan Deborah Samuel.

Matsayar Jamil a kan batun

Matukin jirgin saman ya ce dukkan addinai sun yi hani da batanci ya kuma ya ja kunnen mutane su rika girmama addinan juna.

Kamar yadda ya wallafa:

“A musulunci mu na girmama Injila, Ataura, Zabura da sauran littafai kuma ba ma wulakanta ko wanne addini da kuma ko wanne annabi tun daga Annabi Adam zuwa Muhammad SAW da Qur’ani.
“Hukuncin yin batanci kisa ne a ko wanne addini har da na Kirista. Ku girmama addinan jama’a, abu ne mai sauki.”

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

Wannan wallafar ta Jamil ta janyo cece-kuce.

Karin bayanin da Jamil ya yi

Bayan ganin mutane sun yi ca, Jamil ya yi fashin baki a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter.

Ya ce:

“Ina goyon bayan kisa kuma? Ha! Da gaske ku ke? Na ga yadda ake ta yada magana ta, wai mene ke damun mutane ne? Sunana ya na dadin a kanun labarai ko.
“Na bayyana dokar da ke shimfide da abubuwan da ke faruwa ne. A daina sauya min maganara. Ni musulmi ne, ba na kirkirar dokoki.”

Tsokacin ‘yan Najeriya

Mutane daga na Facebook har Twitter sun dinga surutai akan wallafar ta shi.

@AkpoaredeM ya ce:

“Lokaci ne kafin Ubangiji ya yi aike cikin ‘yan uwansa. Lokaci ba ya karya.”

@iam_methuselah ta ce:

“Duk ‘yan arewa su na da tattsauran ra’ayi. Na yi rayuwa da Larabawa, ba haka su ke ba.”

Kara karanta wannan

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

Sageer Rabiu ya ce:

“Kiristoci sun sauya salon bata wa musulmai rai ta hanyar yin batanci ga addinisu.”

Kinsley N Uzoma ya ce:

“A kasar musulmai ne kadai ake yin hakan, wannan dalilin ne zai sa wajibi ne a raba ‘yan Biafra daga Najeriya.”

Triple Osa Olayodeolawaleleoluseun ya ce:

“Wannan dalilin kadai ya isa NYSC da sauran shirye-shirye da ke hada arewa da kudu su yi gaggawar tsayawa... rayuwa cikin ‘yan arewa ta na da hadari.”

TopTen Balogun ya ce:

“Idan har hukuncin mai batanci kisa ne, shin me ne ne hukuncin makasan? Na gode wa Ubangiji da ni ba Musulmi ba ne.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: