Idan gwamnati bata biyamu N500bn ba, yanzu kuka fara wahalar mai: IPMAN ga yan Najeriya

Idan gwamnati bata biyamu N500bn ba, yanzu kuka fara wahalar mai: IPMAN ga yan Najeriya

  • Yan kasuwan mai sun ce idan gwamnatin tarayya bata biyasu bashin da suke binta ba, za'a yi wahalar man da ba'a taba yi ba
  • Kungiyar IPMAN tace tana bin gwamnati bashin bilyan dari biyar tsawon watanni tara yanzu amma ba'a biyata ba
  • An fara wahalar mai a jihohin Legas, Kano da birnin tarayya Abuja fari daga ranar Litinin

Kano - Kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu watau Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) ta yi gargadin cewa za'ayi wahalar man da ba'a taba yi ba a kasar nan.

IPMAN tace mafita daya tilo itace gwamnatin tarayya ta tilastawa hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA) ta biya ta kudin bashin da take binta N500bn.

Shugaban IPMAN na jihar Kano, Bashir DanMalam ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ranar Litinin, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

Yayi bayanin cewa rashin biyan wannan kudi tsawon watanni tara yanzu ya talauta wasu daga cikin mambobinsu kuma ya tsananta tashin farashin man Diesel.

IPMAN ga yan Najeriya
Idan gwamnati bata biyamu N500bn ba, yanzu kuka fara wahalar mai: IPMAN ga yan Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Danmalam yace:

"Hukumar NMDPRA ke da hakkin biyan kudin nan. Sakamakon rashin biyan kudin tsawon watanni tara yanzu, yan kasuwa da dama sun gaza daukan mai saboda ba'a biyansu."
"Wannan sabon layukan man da kuke gani a Abuja somin tabi ne idan ba'a biyamu ba."
"Bamu ce a kara mana kudi ba; kawai abinda muke so a biyamu kudinmu N500bn."

Danmalam yace tun lokacin da aka soke hukumomin DPR, PEF da PPPRA, sau biyu aka biyasu.

Saboda haka ya yi kira da gwamnatin tarayya ta shiga wannan lamarin kafin yayi muni.

Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya shiga takarar shugaban ƙasa a APC

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Karamin ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya ayyana kudirinsa na shiga tseren takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Tuni dai kungiyoyin magoya baya suka gabatar masa da Fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa na Miliyan N100m a APC.

Haka zalika ƙungiyoyin sun gabatar wa gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba Fom ɗin takara. Tun a baya dai gwamnan ya ayyana shiga takara bayan gana wa da Buhari a Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng