Da dumi-dumi: Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi dala 75,000 a hedkwatar APC

Da dumi-dumi: Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi dala 75,000 a hedkwatar APC

  • Wani barawo ya arce da zunzurutun kudi kimanin naira miliyan 43 a sakatariyar jam'iyyar APC na kasa
  • Lamarin wanda ya afku a ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, ya haifar da yar rudani a tsakanin mutanen da ke wajen
  • Sai dai majiya ta bayyana cewa kudin da aka sace bai da alaka da kudaden da aka siyar da fom din takarar mukaman shugabanci

Abuja - An shiga rudani a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, lokacin da zunzurutun kudi har kimanin naira miliyan 43 ya yi batan dabo.

An tattaro cewa an ruguza babban rumfar da a karkashinsa ake siyar da fom din takara ba tare da wani cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Jaridar Punch ta rahoto cewa jam’iyyar ta yanke shawarar amfani da manyan rumfunar da aka kafa ne saboda aikin gyare-gyare da ake yi a ainahin ginin sakatariyar.

An rahoto cewa kudi dala 75,000 ne ya yi batan dabo a yayin da ake turereniya wajen shiga harabar jam’iyyar.

Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi naira miliyan 43 a hedkwatar APC
Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi naira miliyan 43 a hedkwatar APC Hoto: sunnewsonline.com

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, majiyoyin jam’iyyar sun bayyana cewa kudin da ya bata bai da alaka da kudaden da aka siyar da fom din takara domin ana sanya ran masu takara za su tura kudin ne a asusun bankin da aka tanada don haka kafin su karbi fom dinsu a Buhari House.

Majiyar ta ce:

“$75,000 ne. kun san akwai turereniya a wajen sakatariyar lokacin da yan takara da magoya bayansu ke kokarin shiga ciki.
“Lokacin da damin kudin ya fadi, sai aka neme shi aka rasa a cikin kyaftawan ido. Zuwa lokacin da aka sanar da jami’an tsaro tuni barawon ya arce da takardar kudin.”

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

Sakatariyar jam’iyyar dai ta cika ta tunbatsa yayin da yan takara ke karbar fom din takarar kujerun shugabanci.

Daruruwan magoya baya sun taru a wajen Buhari House domin karfafawa yan takarar da suke goyowa baya gwiwa a hanyarsu ta shiga harabar.

Siyar da fom da aka yi na ranar Laraba ya nuna karara cewa ba lallai ne harabar jam’iyyar ya dauki shirin na kimanin makonni biyu ba.

The Eagle ta rahoto cewa ana kan tattaunawa domin mayar da shirin zuwa wani waje na daban.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, an jiyo jami’an jam’iyyar suna tattaunawa domin mayar da shirin zuwa babbar cibiyar taro na kasa, Abuja.

‘Dan Jam’iyya ya rubutawa Shugabannin APC takarda, yana so a hana Gwamna tazarce

A wani labari na daban, mun ji cewa Ayodele Oludiran wanda yana cikin ‘yan jam’iyyar APC a jihar Ogun, ya kai karar gwamnansa wajen shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan Najeriya ya fusata, ya maka Buhari a kotu saboda gallazawa 'yan Najeriya

Daily Trust ta ce Ayodele Oludiran ya gabatar da korafinsa gaban Sanata Abdullahi Adamu, yana mai jan kunnensa a kan sake ba Gwamna Dapo Abiodun takara.

A cewar Oludiran, zargin da suke kan gwamnan ya sa akwai hadari a ba shi tutar APC a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng