Babbar matsala ta Buhari 1 ne, kuma babu abin da ya tabuka a cikin shekaru 7 inji Yakasai
- Jaridar nan ta Punch ta samu damar yin hira da Salihu Tanko Yakasai wanda ya taba rike mukamai a gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje
- A wannan tattaunawa, Salihu Tanko Yakasai ya yi bayani a game da alakarsa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da abin da ya sa ya tsige shi
- Legit.ng Hausa ta bibiyi wannan hira, ta ji yadda Salihu Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu ya bayyana gazawar gwamnatin Muhammadu Buhari
Salihu Tanko Yakasai ya fahimci dalilin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na tunbuke shi, ba zai yiwu na kusa da shi ya soki gwamnatin tarayya ba.
Ko bayan an kore shi daga ofis, tsohon Darekta Janar din ya ce ya hadu da tsohon mai gidan na sa.
Rashin tsaro a Arewa
A game da sha’anin rashin tsaro, Yakasai ya ce abin bai shafe shi kai-tsaye ba, amma ‘yan bindiga sun hallaka mijin ‘yaruwarsa a gaban iyalinsa a gidansu.
Haka zalika ‘dan siyasar ya bada labarin yadda aka yi garkuwa da wani ‘danuwan surukinsa a Kaduna. Hakan ta sa ya fito ya na tir da gwamnatin APC.
“Babu wani mutum musamman a Arewacin Najeriya da bai san wani wanda matsalar tsaro ta shafe shi ba. Sai mu yi shiru, a cigaba da tafiya a haka?”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun fatattaki gwamnatin PDP ne saboda matsalar Boko Haram a Arewa maso gabas, a yau ‘yan bindiga sun karbe bangaren Arewa maso yamma.”
- Salihu Tanko Yakassai
Inda za a yabawa Buhari
A cewar Dawisu, a bangare daya ne za a iya yabawa gwamnatin Buhari, wajen gina abubuwan more rayuwa, amma bayan nan ya ce bai tabuka komai ba.
“A kan batun tsaro, babu abin da ya yi. A kan tattalin arziki, babu abin da ya yi. A wajen yaki da rashin gaskiya, abubuwa sun fi kyau kafin ya karbi mulki.”
“Ya na kokari wajen gina hanyoyi, amma ina tsaro? Dubi titin Abuja-Kaduna wanda ita ce zuciyar Arewa? Ba za ka iya bin hanyar hankali kwance ba.”
“Ba za ka iya bin jirgin sama ta Kaduna ba; ba za ka iya bin jirgin kasa ba, ba za ka iya bin titi ba. Ana kai hari a titin kusan duk rana, ina amfanin yin titin?”
- Salihu Tanko Yakassai
Mecece matsalar Buhari?
Da aka tambayi tsohon hadimin gwamnan a kan kallon da ake yi wa shugaba Muhammadu Buhari na cewa ya samu mugayen fadawa, ya yi na’am da hakan.
“Matsala ta da shi (Buhari) kusan bai iya tabuka komai; bai jan kunen mutanensa, kuma bai tsaya tsayin-daka kan mutanen da ya ba mukami a gwamnatinsa ba.”
“Ana saba masa, amma ya gagara daukar mataki. Ina tunani babbar matsalarsa ita ce dabi’arsa – na rashin iya daukar mataki, ya tsoma baki inda ya dace.”
Salihu Tanko Yakassai
Asali: Legit.ng