Ramadaniyyat 1443: Duk Rayuwar da Babu Allah A Cikinta Mai ƙunci Ce, Sheikh Dr Sani Umar R/Lemo

Ramadaniyyat 1443: Duk Rayuwar da Babu Allah A Cikinta Mai ƙunci Ce, Sheikh Dr Sani Umar R/Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

A cikin jeringiyar janyo hankali na watar Ramadana da Malam ya yiwa lakabi da Ramadaniyyat, ya yi tsokaci kan rayuwar da babu Allah cikinta.

Duk Rayuwar da Babu Allah A Cikinta Mai ƙunci Ce

1. Allah (SWT) yana cewa:

“Wanda kuma ya bijire wa Alƙur’ani to lalle zai yi rayuwa mai ƙunci, kuma Mu tashe shi makaho ranar alƙiyama.” [Da Ha, 124].

2. Duk wanda ya bijire wa karantarwar Allah to ba shi babu samun nutsuwa ko yalwar ƙirji a duniya, zai rayu ne cikin ƙuncin vata da kiɗimewar tunani da rahin nutsuwar ƙwaƙwalwa da yawan dogayen burace-burace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bayan Shekara biyu, Buhari ya amince yan Najeriya su je masa Barka da Sallah, an gindaya sharuɗda

Ko da kuwa za a ga alamun jin daɗi a zahirinsa; yana saka tufafin da ya ga dama, ya ci abin da ya so, ya zauna inda ya so; zuciyarsa za ta ci gaba da rayuwa cikin damuwa da ɗimuwa.

Zai dai riƙa lulluve damuwarsa ne da mayen son duniya da son shugabanci in bai ma haɗa da mayen shaye-shaye ba, domin zautuwar da take cikin waɗannan al'amura ta fi ta kayan maye.

Domin idan ɗan maye ya bugu yakan farfaɗo, amma wanda son duniya da son shugabanci suka zautar da shi, to ba ya farfaɗowa sai sanda ya ji shi cikin likkafani.

3. To hakanan irin wannan ƙuncin rayuwa zai ci ga ba da kasancewa tare da shi, ba zai su rabu ba har sai ranar da ya shiriya ya komo ga Allah mahaliccinsa, ko kuma su ci gaba da kasancewa tare har zuwa ƙabarinsa, daga nan ƙunci ya ci gaba da lizimtarsa har zuwa makomarsa Jahannam. Allah Ya tsare mu.

Kara karanta wannan

2023: Sabon ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayyana aniyarsa a APC, ya nemi a rage masa kuɗin Fom

4. Don haka babu yadda farin ciki da nutsuwar zuciya za su samu ga mutum sai ya rungumi shiriyar Allah Mahaliccinsa, abin bautarsa na gaskiya, ya tabbatar da cewa, duk wani abin bauta ba shi ba ƙarya ce. Wannan ita ce hanya ɗaya tilo ta samun arzukin duniya da na lahira.

Allah ya sa mu dace. Amin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel