Jaridar Legit.ng ta shiga jerin fitattun masu mawallafa labarai a Facebook na duniya

Jaridar Legit.ng ta shiga jerin fitattun masu mawallafa labarai a Facebook na duniya

Fitacciyar kafar yada labaran zamani a Najeriya, Legit.ng ta kara habaka matsayinta na kan gaba a Facebook tare da samun mabiya sama da miliyan 14 a watan Maris da jimillar labaran da ta wallafa sama da 4,264.

A karshen kwatan farko na 2022, Newswhip ta sake ambatan Legit.ng a cikin manyan mawallafan labarai a Facebook guda 5 a duniya

Shahararriyar kafar yada labarai da nishadantarwa ta Najeriya, kuma lamba 1, Legit.ng ta buge kafar labaran kasar Amurka wato CNN daga matsayi na 5 da ta rike a baya, tare da zagayen dangwale, sharhi, karatu da sauransu a Facebook da lambobi 14,636,032 da kuma labarai 4,264.

Shakka babu, wannan tabbaci ne ga duniya cewa, Legit.ng ce kan gaba wajen ilmantarwa, nishadantarwa da kuma kawo sahihan labarai ga ilahirin 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Dakarun hadin gwiwa sun yi gagarumin nasara: Sun kashe kwamandojin ISWAP 10 da mayaka 100 a tafkin Chadi

Jaridar Legit.ng ta shiga cikin jerin fitattun masu mawallafa labarai a Facebook na duniya
Jaridar Legit.ng ta shiga cikin jerin fitattun masu mawallafa labarai a Facebook na duniya
Asali: Original

Legit.ng ta biyo bayan manyan kafafen yada labarai na duniya, kamar su Dailywire, Dailymail, Mirror da BBC, a cikin jerin da Newship Analytics ya fitar a watan Maris.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka tantance gidajen yada labarai

Tantancewar ta dogara ne ga labaran da aka buga da yaren Ingilishi daga shafukan yada labarai, kuma ana tantancewa ta hanyar dangwale, sharhi da yada labaran a shafukan Facebook, wanda ta nan ake gane matsayin kowace jarida.

Kan gaba wajen yada labarai

Legit.ng na ci gaba da jan ragamar kafafen yada labarai kamar yadda wani rahoto da aka buga kwanan nan ya nuna cewa kafar na yana daya daga cikin shafukan Facebook da suka fi daukar hankali a nahiyar Afirka.

Kasance cikin jerin mabiyanmu da miliyoyin masu karanta labaranmu masu nagarta

Legit.ng (Tsohuwar Naij.com) ita ce mafi girma a wajen buga labarai a Najeriya (inji Alexa Rank).

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Kowane wata, mutane 10M+ ke ganin labaranta yayin da akalla mutum 50M ke karanta su akan kafar yanar gizo.

Jaridar Legit.ng na da mabiya a shafukan sada zumunta na Facebook da yawansu ya kai miliyan 11.4 a dukkan shafukanta, wanda akalla labari daya ke isa ga mutane 80,000.

Idan ka kasa 'yan Najeriya da ke hawa Facebook, na 4 ciki na bibiyan shafin Legit.ng.

A matsayinta na babbar mai wallafa labarai a kasar nan, Legit.ng tana da alhakin inganta rayuwar masu karata labaranta ta kowace hanya.

Shi ya sa muke alfahari da kanmu wajen samar da labarai masu canza rayuwa da ke sa masu karatunmu su kara fahimtar duniyar da ke kewaye da su ta hanyoyi da yawa..

Asali: Legit.ng

Online view pixel