Duk magidancin cocina da ke dukan matarsa, sai na lakada masa duka, Fasto Suleman

Duk magidancin cocina da ke dukan matarsa, sai na lakada masa duka, Fasto Suleman

  • Fitaccen fasto, Apostle Suleman, ya gargadi mazan cocinsa kan dukan mata inda yace da kansa zai lakada musu duka idan ya samu labarin sun duka matansu
  • Faston ya yi Allah wadai da halayyar maza sakarkaru wadanda suke gwada karfi kan mata a maimakon kwaba musu da baki kuma su dauka
  • Ya koka da 'yan uwa maza na matan, wadanda ba su shiryawa su rama wa 'yan uwansu mata dukan da maza ke musu a gidajen aure

Babban faston cocin Omega Fire Ministries International, Apostle Johnson Suleman, ya ce zai tabbatar da cewa duk wani magidancin cocinsa da ke dukan matarsa, shima ya lakada masa bakin duka.

Punch ta ruwaito cewa, ya sanar da hakan yayin da ya shawarci mata da su tsere su bar duk auren da ake cin zarafinsu tun suna da ransu inda ya kara da cewa wadanda suka zauna kuwa za a birne su idan sun mutu sakamakon cin zarafi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

Duk magidancin cocina da ke dukan matarsa, sai na lakada masa duka, Fasto Suleman
Duk magidancin cocina da ke dukan matarsa, sai na lakada masa duka, Fasto Suleman. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Apostle Suleman ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi ga mabiyansa ana tsaka da labaran mutuwar mawakiyar yabo, Osinachi Nwachukwu, wacce ake zargin cin zarafin da mijinta ke mata ne ya kashe ta.

Ya ce:

"A lokacin da nace akwai wasu irin aure da ya dace a raba, babu abinda ba a ce a kaina ba. Saboda haka nayi shiru, ko kun sake jin na fadi wani abu?
"Amma yanzu haka kowa ke fadi. Wani ya zo wurina yana cewa 'a lokacin da ka fadi shekarun da suka gabata ai zaginka aka dinga yi."

A rahoton Daily Trust,

Ya cigaba, "Duk matan nan da mazansu ke dukansu, ba su 'yan uwa maza ne? Idan basu da 'yan uwa maza na jini, suna da 'yan uwa maza Kiristoci.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

"Idan kana cocin nan kuma kana dukan matarka, ka daina. Idan ta kawo ka kara wurina, za mu zane ka.
"Zan je ofishin 'yan sanda in samu yardarsu kafin in tattara maza a cocin nan su zane ka."
Ya kara da cewa, "Sakarkarun maza ne kadai ke dukan mata. Ta yaya ka samu matar? Ku yi magana. Ta yaya za ka aje ta? Ku fadi. Da baki ake juya mace ba wai da hannu ba."

Ramadan: Magidanci ya lakada wa matarsa mai ciki mugun duka kan abincin Sahur

A wani labari na daban, wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Taofeek Gbolagade, a safiyar Talata, ya nadawa matarsa mai juna biyu, wacce aka boye sunanta, dukan kawo wuka saboda ta gaza girka masa abincin sahur.

Vanguard ta gano yadda lamarin ya auku misalin karfe 4:00 na asuba a gidansu dake cikin rukunnan gidajen Ogbere cikin Ibadan na jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Dan majalisa a Filato: An kashe makusantana fiye da 50 a harin 'yan bindiga

Wani ganau ya ce: "Wannan mutumin ya saba dukan matarsa a kan duk wani karamin sabanin da suka samu. Yau dai na fahimci abunda ya faru. Shi musulmi ne, saboda haka ina tunanin sun yi sa-in-sa a kan abincin Sahur. "

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng