Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157
- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi afuwa wa wasu fursunoni 159 dake garkame yanzu haka a kurkuku a fadin tarayya
- Daga cikin wadanda aka yafewa akwai manyan tsaffin Sojoji da aka garkame kan yunkurin juyin mulki
- Tsaffin shugabannin kasa, gwamnoni da shugaban kasa ne suka yanke wannan shawara
Abuja - Majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku yanzu.
Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.
Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC
Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifi a hannu cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.
A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, an yafewa tsaffin gwamnonin biyu ne bisa lafiya da yawan shekarunsu.
Jolly Nyame, wanda tsohon gwamnan Taraba ne tsakanin 1999 da 2007, na zaman shekaru 12 da kotu ta yanke masa a Kurkukun Kuje kan laifin almundahanar dukiyar jama'a.
Shi kuma Joshua Dariya, wanda tsohon Gwamnan Plateau ne tsakanin 1999 da 2007, na zaman kurkuku ne kan laifin satan N2bn na kudin jama'arsa.
Kotu ta yanke masa hukunci a Yunin 2018, lokacin yana ofis matsayin Sanata mai wakiltan Plateau ta tsakiya.
Buhari ya kira zaman dukkan masu mulki da tsaffin shugabannin Najeriya
Dazu mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron masu ruwa da tsaki da tsaffin shugabannin Najeriya.
Wannan shine karo na hudu da Buhari zai kira wannan zama tun da ya hau mulki.
Na karshe da aka yi shine na Agustan 2020 yayinda cutar Korona tayi sauki.
Wadanda ke hallare sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha; NSA Babagana Munguno da Farfesa Ibrahim Gambari.
Tsaffin Shugaban kasan dake hallare a wajen sun hada Abdusalami Abubakar; Yakubu Gowon da Goodluck Jonathan.
Sauran na hallara ta yanar gizo.
Gwamnoni dake hallare da kafafunsu sun hada da Kayode Fayemi (Ekiti); Hope Uzodinma (Imo) ; Atiku Bagudu (Kebbi); Bello Matawalle (Zamfara); Nasir El-rufa’i (Kaduna); Abdullahi Ganduje (Kano) da Abubakar Badaru (Jigawa).
Asali: Legit.ng