Buhari ya bada izinin fitar da ton 40,000 na kayan hatsi daga rumbun gwamnati don bikin Easter da Azumi

Buhari ya bada izinin fitar da ton 40,000 na kayan hatsi daga rumbun gwamnati don bikin Easter da Azumi

  • Yayinda aka sanar da ranar hutun Easter, Buhari ya ce a fitar da buhuhunan hatsi don bikin Easter, Azumi da Sallah
  • Wannan na zuwa ne bayan kwanaki goma sha biyu da mabiya addinin Islama suka shiga watar azumi
  • Cikin ton 40,000 da za'a saki, za'a baiwa ma'aikatar Hajiya Sadiya Farouq ton 12,000 don rabawa yan gudun hijra

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin fitar da kayan hatsi ton 40,000 daga rumbun kayan masarufin gwamnati don taimakawa talakawa wajen murnin bikin Easter, azumi da Sallah.

Ministan noma da raya karkara, Muhammad Mahmoud, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa Mahmoud ya gaba da Buhari ne ranar Talata, 12 ga Afrilu, 2022.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Sanar Da Ranakun Hutun Easter Na 2022

A cewarsa, sakin wadannan kayan hatsi zai rage farashin kayan masarufi a kasuwa.

Buhari
Buhari ya bada izinin fitar da ton 40,000 na kayan hatsi daga rumbun gwamnati don bikin Easter da Azumi Hoto: Presidency
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa cikin ton 40,000 da za'a saki, za'a baiwa ma'aikatar Hajiya Sadiya Farouq ton 12,000 don rabawa yan gudun hijra dake fadin tarayya.

Yace:

"(Buhari) ya umurceni na fitar da kayan hatsi daga rumbun gwamnati na ma'aikatar noma da raya karkara."
"Za'a yi hakan ne domin rage zafin hauhawan farashin kaya a fadin tarayya. Hakan zai rage farashin kaya don mutane dake shirin Ramadan, Easter da Sallah."

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Sanar Da Ranakun Hutun Easter Na 2022

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Juma'a da Litinin a matsayin hutu don murnar bukukuwan Easter a kasar.

Easter biki ne da mabiya addinin Kirista ke yi domin murnar dawowar Annabi Isah (AS) bayan an giciye shi kuma ya mutu.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng