Daga shiga ofis, Gwamna ya nada mutanen da za su sasanta da duk wani 'Dan ta’adda

Daga shiga ofis, Gwamna ya nada mutanen da za su sasanta da duk wani 'Dan ta’adda

  • Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya na kokarin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Anambra
  • Gwamnan ya kafa kwamiti da zai saurari abin da ya jawo IPOB da makamantansu suke tada fitina
  • Wadanda ke cikin kwamitin su ne Bianca, Farfesa Odinkalu, Nyesom Wike, da su Dr. Joe Abbah

Anambra - Mai girma gwamna Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra, ya kafa wani kwamiti da ake sa ran zai kawo zaman lafiya a kasar Ibo.

Jaridar Tribune ta ce kwamitin da Charles Chukwuma Soludo ya kafa domin a sasanta da ‘yan ta’adda zai yi aiki ne a karkashin Farfesa Chidi Odinkalu.

A yayin da Chidi Odinkalu zai jagoranci kwamitin mai suna ‘Truth, Justice and Peace Committee’, Ambasada Bianca Ojukwu aka zaba a matsayin sakatare.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan Anambra ya ba Buhari shawarar abin da ya kamata ayi wa Nnamdi Kanu

Sakatariyar kwamitin, Amb. Bianca Ojukwu wanda mai daki ce wajen Marigayi Odumegwu Ojukwu ta taba zama babbar Jakadar Najeriya zuwa kasar Sifen.

Solo Osita Chukwulobelu ya fitar da jawabi

Wannan sanarwa ta fito ne ta bakin sakataren gwamnatin jihar Anambra, Farfesa Solo Osita Chukwulobelu wanda ya fitar da jawabi a babban birnin Awka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Chalres Soludo
Gwamnan Anambra, Charles Soludo Hoto: CCSoludo
Asali: Twitter

Aikin kwamitin shi ne kawo karshen matsalar tsaro ta hanyar yin gaskiya da yi wa kowa adalci. 'Yan kwamitin za su zauna da duk mai tada zaune-tsaye.

Farfesa Chukwulobelu ya ce wannan kwamiti zai yi aiki ne kai-tsaye da gwamna, kuma za a ba su tsawon watanni shida domin su iya karkare aikin na su.

Su wanene 'yan kwamitin

The Nation ta ce ragowar 'yan kwamitin su ne; Charles Oputa, Dr. John Otu, Ngozi Odumuko, Ms Onyeka Onwenu, Dr. Joe Abah, sai Chukwuma Okpalaezukwu.

Kara karanta wannan

2023: Wike ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa wajen Janar Babangida da Abdussalami

Sauran ‘yan wannan kwamitin sun hada da; Dr. Joe Nwaorgu, Dr. Udenta Udenta, Dr. Uju Agomoh, Rabaren Jerome Madueke da Dr. Okechukwu C. Obi-Okoye.

Har ila yau akwai Sam Evwuatu da kuma Farfesa Joseph Ikechebelu a cikin wannan kwamitin.

A fito da Nnamdi Kanu - Soludo

A jiya ne aka ji cewa Gwamnan Anambra, Charles Chukwuma Soludo ya na kokarin kawo zaman lafiya a jiharsa, don haka ya bada shawarar a fito da Nnamadi Kanu.

Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya bude kofar sulhu da ‘yan ta’addan da su ka addabi kudu maso gabas, Gwamnan ya hada kai ne da limamai da kuma sarakuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng