'Yanuwan BOA MD sun biya N100m kafin ya bar hannun miyagun da suka tare jirgin kasa

'Yanuwan BOA MD sun biya N100m kafin ya bar hannun miyagun da suka tare jirgin kasa

  • Ashe ba haka nan kurum ‘yan bindiga su ka saki shugaban bankin manoma na kasa da ke tsare ba
  • Alhaji Alwan Hassan ya na cikin wadanda aka yi awon gaba da su da aka tare jirgin Kaduna-Abuja
  • ‘Yan bindiga sun ce saboda tsufarsa ya samu ‘yanci, amma ‘yanuwan Dattijon sun ce sun biya N100m

Kaduna - Shugaban bankin manoma na kasa watau BOA, Alwan Hassan ya samu ‘yanci daga hannun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su kwanan baya.

Wata majiya ta shaidawa Daily Nigerian cewa sai da ‘yanuwan wannan Bawan Allah suka biya fansar har Naira miliyan 100 kafin ‘yan ta’addan su fito da shi.

Alwan Hassan ya shafe kusan kwana tara a tsare, tun bayan da aka kai hari a hanyar jirgin kasan Kaduna-Abuja, aka yi garkuwa da wasu daga cikin matafiya.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga za su ‘kashe’ fasinjojin jirgin kasa, idan Gwamnati ta gaza biya masu bukata

‘Yanuwa da dangin Darektan bankin na BOA sun kai fansar Naira miliyan 100, kafin ya kubuta. Kamar yadda aka ji, wasu miyagu su ka karbi kudin a Kaduna.

Wani ‘danuwan Hassan ya shaidawa jaridar cewa ‘yan bindigan sun aiko masu faifen bidiyon irin wahalar da yake sha tare da sauran mutane a kungurmin jeji.

BOA MD
Shuganan BOA, Alwan Hassan Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka yi inji 'danwansa

“Kwanakin baya su ka turo mana wani bidiyon halin ni ‘ya su da suke ciki domin su iya samun abin da suke bukata.”
“Alwan cewa kurum yake yi ‘ku ba su duk abin da su ka bukata.’ Saboda haka aka biya abin da suka nema.” - 'danuwansa

Rahoton ya bayyana cewa da farko ‘yan ta’addan sun ce a kai kudin cikin wani jeji ne a Katsina. A ranar Talata kuma su ka bukaci a kawo su wani dajin a Kaduna.

Kara karanta wannan

Cikakkiyar hudubar Juma’ar da ta jawo aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Apo

Majiyar ta ce bayan an ci tafiya na sa’o’i, sai wasu ‘yan bindiga rututu su ka zo su ka karbi kudin.

Wannan haka ya ke -Audu Bulama Bukarti

Audu Bulama Bukarti wanda masani ne a kan harkar tsaro, ya tabbatar da wannan magana a shafinsa na Facebook, ya ce tabbas an fada masa an biya fansa.

A cewar Audu Bulama Bukarti, kudin da 'yan ta'adda su ke samu kullum kara yawa yake yi, sannan kuma abin takaicin shi ne hukumomi sun gaza yin komai.

Saboda shekarunsa mu ka sake shi - 'Yan bindiga

Legit.ng Hausa ta kawo labari ‘yan ta’addan su na ikirarin cewa ba a biya kudi kafin a saki wannan mutumi ba, amma bayanai su na nuna akasin wannan.

‘Yan ta’addan da suka kai hari ga jirgin kasan Kaduna-Abuja sun yi magana a wani bidiyo da ya fito jiya, su na cewa dole ne gwamnati ta biya masu bukatunsu.

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng