Sojoji sun dakile mota dauke da N100m kudin fansa za'a kaiwa yan bindiga
- Yayinda ake kokarin kaiwa yan bindiga kudin fansa milyan dari, Sojoji sun tsare motar dake dauke da kudin
- Bidiyon wasu Sojoji da suka kama motar ta bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta
- Mutane da dama sun tofa albarkatun bakinsu inda wasu suka ce babu amfanin kama kudin tun da ba ceto wanda aka sace zasu yi ba
Jami'an hukumar Sojin Najeriya sun yi arangama da wata mota dauke da miliyoyin naira da kiret din kwai za'a kaiwa yan bindiga matsayin kudin fansa.
A bidiyon dake yawo a kafafen ra'ayi da sada zumunta, an ji wani soja na cewa milyan dari aka samu cikin mota mai lambar Kano ‘FGE-959TC’.
Sahara Reporters da ta saki bidiyon tace ba tada tabbacin lokacin da aka dauki bidiyon.
Daya daga cikin Sojin yace:
"Duka kudi ne, zasu kaiwa yan bindiga, ko jakar nan, duka kudi ne, wannan kwalayen indomien duka kudi ne."
"Kudi ne cike da motar gaba daya, N100 million fa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli bidiyon:
'Yanuwan BOA MD sun biya N100m kafin ya bar hannun miyagun da suka tare jirgin kasa
Shugaban bankin manoma na kasa watau BOA, Alwan Hassan ya samu ‘yanci daga hannun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su kwanan baya.
Wata majiya ta shaidawa Daily Nigerian cewa sai da ‘yanuwan wannan Bawan Allah suka biya fansar har Naira miliyan 100 kafin ‘yan ta’addan su fito da shi.
Alwan Hassan ya shafe kusan kwana tara a tsare, tun bayan da aka kai hari a hanyar jirgin kasan Kaduna-Abuja, aka yi garkuwa da wasu daga cikin matafiya.
‘Yanuwa da dangin Darektan bankin na BOA sun kai fansar Naira miliyan 100, kafin ya kubuta. Kamar yadda aka ji, wasu miyagu su ka karbi kudin a Kaduna.
Wani ‘danuwan Hassan ya shaidawa jaridar cewa ‘yan bindigan sun aiko masu faifen bidiyon irin wahalar da yake sha tare da sauran mutane a kungurmin jeji.
Asali: Legit.ng