‘Yan bindiga za su ‘kashe’ fasinjojin jirgin kasa, idan Gwamnati ta gaza biya masu bukata
- Miyagun ‘yan ta’addan da suka kai hari ga jirgin kasan Kaduna-Abuja sun yi magana a wani bidiyo
- ‘Yan bindigan sun bayyana ne yayin da suka saki shugaban bankin manoma (BOA), Alwan Hassan
- An ji ‘yan ta’addan da ake zargin su na cikin jejin Kaduna su na cewa ba su bukatar a biya su kudi
Kaduna - ‘Yan bindigan da suka dasa bam a hanyar jirgin kasa, su ka yi awon-gaba da Bayin Allah su na barazanar cewa za su kashe mutanen da ke hannunsu.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu 2022, inda aka ji cewa wadannan ‘yan ta’addan su na gargadin gwamnatin tarayya.
A wani gajeren faifen bidiyo da ya bayyana a jiya, an ji ‘yan bindigan su na cewa ba kudi ne a gabansu ba. Akasin yadda aka saba ji idan an dauke mutane.
Kamar yadda suka bayyana, wadannan ‘yan bindiga sun ce gwamnati ta san abin da suke nema.
Alwan Hassan ya kubuta
“Mu ne gungun wadanda mu ka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa kwanakin baya. Daga ciki har da wannan mutumi da ya roki mu kyale shi saboda shekarunsa.”
“Sai mu ka ji tausayinsa, ganin cewa watan Ramadan ya zo, za mu so mu mika shi ga iyalinsa.” - Wani 'Dan ta'adda
Wadannan ‘yan ta’adda sun ja-kunnen gwamnati da cewa ka da ta rudu ganin an saki wannan Bawan Allah, domin sun yi hakan ne kurum la’akari da tsufansa.
"Kashe su ba wani wahala ba ne"
“Ina so in jaddada cewa abin da ya fada gaskiya ne. Ka da ku nemi bincikenmu, ko kokarin ceto su domin hallaka su ba wani abu ne mai wahala a wajenmu ba.”
“Ba mu son kudinku, da kudi mu ke nema, da ba mu kai harin ba. Kun san abin da mu ke bukata.”- Wani 'Dan ta'adda
Ana zargi su na dajin Birnin Gwari
Daily Trust ta na tunanin an dauki wannan bidiyon ne a wani sansani da ‘yan ta’adda da suka tare a yankin Polwire, a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Ana iya ganin wata tan-tan (APC) wanda ‘yan bindiga su ka kona a makon nan a bidiyon. Hakan ya tabbatar da cewa wadannan mutane su na jejin Birnin Gwari.
Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan bidiyo na kusan minti daya da rabi, inda aka ji wani cikin ‘yan ta’addan ya na rangada jawabi da harshen Hausa da kyau.
Asali: Legit.ng