Gwamnati ta bankado yadda ma’aikata 1,500 suka shiga aiki ta bayan-fage a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta ce akwai ma’aikata 1, 500 da suke amfani da takardun samun aiki na bogi
- Shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya, Folashade Yemi-Esan ta bada wannan sanarwar a taro
- ICPC da hadin kan ofishin ma’aikatan gwamnatin tarayya ne su ke kokarin tono marasa gaskiya
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta gano sama da ma’aikata 1, 500 da suka gabatar da takardun samun aiki na bogi a gaban kwamitin tantance ma’aikata.
Kamar yadda Channels TV ta fitar da rahoto a ranar Talata, 5 ga watan Afrilu 2022, shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya ce ta yi wannan jawabi a jiya.
Folashade Yemi-Esan ta yi magana a taron ‘National Policy Dialogue on Entrenching Transparency in Public Office Recruitment in Nigeria’ da aka yi.
Hukumar ICPC ta shirya wannan taro ne a garin Abuja domin tabbatar da gaskiya a wajen aiki.
Yemi-Esan ta shaidawa jama’a cewa gwamnatin tarayya ta tsaida albashin ma’aikatanta 3, 000 da suka ki bayyana a gaban kwamitin domin a iya tantance su.
Gidan talabijin ya rahoto Folashade Yemi-Esan ta na cewa makasudin yin wannan bincike shi ne a gano waanda aka ba aikin gwamnati ta bayan fage a Najeriya.
Akwai wasu ma’aikatan da takardun bogi su ke amfani, kuma su na cin kudin gwamnatin tarayya.
Jawabin Folashade Yemi-Esan
“A watan Maris na 2021, ofishin nan (OHCSFNGR) ya sanar da ICPC cewa akwai mutane da-dama masu takardun samun aikin bogi su na ma’aikatu.”
“A wannan lokaci, mun gano cewa a wata ma’aikatar tarayya daya kurum, akwai sama da mutane dubu da ke amfani da takardun samun aiki na karya.”
“Kuma su na cikin wadanda aka sa su a cikin lissafi, ana biyan su albashi duk wata.” - Yemi-Esan
An tono ma'aikatan bayan-fage 500
An ji cewa a wani rahoton dabam wannan karo, ofishin OHCSFNGR ya samu sunayen ma’aikata 500 da ke ma’ikatu da-dama da ke dauke da takardun aikin bogi.
Punch ta ce wannan taron ya samu halartar Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola da wasu manya irin Farfesa Olatunde Babawale da kuma Farfesa Isaac Obasi.
Zulum ya yi yayyafi a Borno
A ranar Talata aka ji cewa Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya bada sanarwar yi wa wasu ma’aikata karin albashi saboda shigowar watan Ramadan.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce ma’aikatan da ke karbar N10, 000 a wata za su samu karin 200% a kudinsu. Bayan haka ya raba masu kayan abinci da kudi.
Asali: Legit.ng