Bidiyon wani mutum da ya rasa hannu, ido, kunne kuma 'dansa ya rasa hannu da kafa a hadarin mota
- Wani bidiyo mai ratsa zuciya ya nuna wani dan Najeriya mai suna Malaolu Oluseye yana bayanin halin da ya shiga bayan mumunan hadari
- Mutumin wanda ma'aikacin Welda ne ya yi bayanin yadda ya rasa idonsa da hannunsa a mumunan hadarin mota a 2019
- Wannan hadari ya shafi 'dansa wanda ya rasa hannunsa kuma ya samu mumunan rauni a kafarsa
Jihar Ogun - Wani dan Najeriya mai suna Malaolu Oluseye ya bayyana a wani bidiyo mai rasta zuciya kan yadda ya rasa sassan jikinsa sakamakon hadarin mota.
Mutumin dan asalin Idi-Ori a jihar Ogun.
Mutumin cike da takaici cikin bidiyon, ya ce gaba daya rayuwarsa ta canza sakamakon hadarin motar kuma yaronsa na cikin wani hali mara kyau.
Ya rasa hannunsa da idonsa a hadarin kuma tun lokacin rayuwarsa ta canza.
Malaolu yace shi da ba zai damu da rashin idonsa da hannunsa ba da abin bai shafi yaronsa ba.
Shi ma yaron ya rasa hannu da kafa
Bidiyon da @bbcnewspidgin ta daura a shafin Instagram ya nuna lokacin da yake tafiya da sandar guragu saboda lalacewar kafarsa.
Matashin yace har yanzu yana jin radadin ciwon.
Mutumin yace:
"Abinda wannan hadari ya janyo min na kona min rai. Ya kwace min ido, hannu daya da kunne. Kuma ya kwacewa 'dana kafa."
Duk da halin da yake ciki, mutumin bai yi kasa a gwiwa ba yana cigaba da aikinsa na welda.
Kalli bidiyon:
Tsokacin yan Najeriya
Yusuf Kunyima yace:
Allahu Akbar Allahu Akbar Allah Mai girama Allah Wanda ya halichi sama da kasa Allah kawo Mana agaji ya Allah Nigeria gabadiya ya Allah
Asali: Legit.ng