Gwamnatin Buhari ta kashe Naira Biliyan 157 a aikin gina babbar gadar Neja-Delta
- Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta ziyarci inda ake aikin gadar ‘Second Niger’
- Zainab Ahmed ta ce gwamnati ta kashe N157bn a kan wannan aiki da zai lamushe fiye da N200bn
- Hukumar NSIA ta Nigerian Sovereign Investment Authority ce ta ke daukar nauyin kwangilar nan
Abuja - Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce kawo yanzu an batar da kudi har N157bn a aikin gadar nan ta Second Niger.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Ministar ta na wannan jawabi yayin da ta ziyarci wajen wannan aiki tare da shugabannin hukumar NSIA ta kasa a ranar Asabar.
Zainab Ahmed ta kai ziyara domin ganin yadda aikin yake tafiya ne tare da Farouk Gumel da Uche Orji wanda shi ne babban darektan NSIA da ke wannan aiki.
Hukumar Nigerian Sovereign Investment Authority ta ba kamfanin Julius Berger Nigeria Plc wannan katafaren aiki da ake sa ran za a gama a Agustan 2022.
Rahoton ya ce Julius Berger Nigeria Plc za su gina gada mai tsawon kilomita 1.6 a kan ruwan Neja, sannan za a gina kananan gadoji biyu da za su ratsa kauyuka.
Daga cikin wannan aikin kuma akwai rusa gadar saman da ake da ita a kan titin Onitsha-Owerri.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Aiki zai ci sama da N200bn
Da ta ke zantawa da manema labarai bayan ta ganewa idanunta, Ministar tarayyar ta ce aikin wannan gada ta fita zakka a kan kowane aiki domin ta ci N206bn.
“A yau mun iya ware N157bn domin wannan aikin, kuma na zo ne domin ganin inda duk kudin nan su ke tafiya.”
“Yau rana ce mai muhimmanci domin ana hada gabar gadojin, kuma wannan shi ne rukunin karshe na karasa gadar.”
-Zainab Ahmed
An yabawa wannan kwangila
Ahmed ta ce ‘yan kwangila su na aiki a kullum dare da rana domin ganin aikin ya kammala. A sanadiyyar aikin, mutane 20, 000 sun samu hanyar cin abinci.
Vanguard ta ce shugaban majalisar da ke kula da aikin NSIA na kasa, Farouk Gumel ya tofa albarkacin bakinsa, ya yaba da yadda muhimmin aikin ke tafiya.
NSIA ce kuma ta bada aikin gyara da fadada titin Abuja-Kaduna-Kano da na hanyar Lagos-Ibadan.
Kwangilar tsare jirgin kasa
Ku na da labari cewa bincike ya nuna Rotimi Amaechi ya so ne a bada kwangilar biliyoyi ga wani karamin kamfanin da bai wuce shekara biyu da kafuwa a Duniya ba.
Ministan sufurin ya yi ta babatu a kan kin amincewa da wannan aiki, amma ya gagara yi wa FEC cikakken bayani, ya dage sai an ba kamfanin Mogjan Nigeria Ltd aikin.
Asali: Legit.ng