Labari da duminsa: Gwamna Ganduje ya mika mulki hannun mataimakinsa, ya shilla kasar waje

Labari da duminsa: Gwamna Ganduje ya mika mulki hannun mataimakinsa, ya shilla kasar waje

  • Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya mika jagorancin Kano hannun mataimakinsa Nasiru Gawuna
  • Bayan kammala taron majalisar zartarwa ta Kano a Abuja, Ganduje ya nufi ƙasar Larabawa halartar wani taron zuba jari
  • Rahoto ya nuna cewa Ganduje ya jima ba shi a cikin Kano, ya taka muhimmiyar rawa a babban taron APC da aka gama

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa mulkin Kano hannun mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ganduje ya yi haka ne jim kaɗam kafin ɗagawar Jirginsa zuwa haɗaɗɗiyar daular larabawa (UAE) ranar Laraba a Abuja.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba.

Gwamna Ganduje da Nasiru Gawuna.
Labari da duminsa: Gwamna Ganduje ya mika mulki hannun mataimakinsa, ya shilla kasar waje Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Ya ce gwamna Ganduje zai halarci taron zuba hannun jari da kungiyar gwamnonin Najeriya NGF ta shige gaba a ƙasar Larabawa, bisa haka Gawuna zai zama muƙaddashin gwamna.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin koma baya, Ɗan takarar gwamna ya yi murabus

Sanarwan ta kuma umarci kwamishinoni, shugabannin ma'aikatu, daraktoci da sauran ƙusoshin gwamnati da sauransu, su ba muƙaddashin gwamna goyon baya da haɗin kai.

Haka nan kuma ta yi bayanin cewa duk wani lamari da ake bukatar sa hannun gwamna a miƙa shi ofishin mataimakin gwamna.

Tun yaushe Ganduje ya bar Kano?

Rahoto ya nuna cewa Ganduje ya jima ba shi a Kano na tsawon lokaci, kuma ya taka muhimmiyar rawa a gangamin APC na ƙasa da aka kammala kwanan nan.

Ko a wannan makon, taron majalisar zartarwa na gwamnatin jihar Kano ya gudana ne a gidan gwamna dake Asokoro, babban birnin tarayya Abuja.

Bayan kammala taron ne mai girma gwamna ya kama hanyar zuwa UAE bayan miƙa ragamar komai hannun Nasiru Gawuna.

A wani labarin kuma Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa

Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya kammala aikinsa ya mika ragamar tafiyar da APC hannun sabon shugaba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa

Sanata Abdullahi Adamu, ya karɓi jagorancin APC a Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa ranar Laraba, 30 ga watan Maris, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262