‘Dan takarar 2023 ya tsaida kamfe na tsawon kwanaki saboda harin da aka kai a jirgin kasa
- Anyim Pius Anyim ya fitar da jawabi bayan samun labarin an kai hari a jirgin kasan Kaduna-Abuja
- Jawabin ya fito ne ta hannun mai magana da bakin kwamitin yakin neman zabensa, Ahmed Buhari
- Sanata Pius Anyim ya yi Allah-wadai, sannan ya ce ba zai fita yawon siyasa gaba daya makon nan ba
Abuja - Sanata Anyim Pius Anyim ya yi tir da harin da aka kai wa matafiya a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto dazu.
Sanata Anyim Pius Anyim wanda ya na cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya ce akwai dabbanci da rashin tausayi a harin da aka kai.
Tsohon shugaban majalisar ya bayyana haka a jawabin da ya fitar ta hannun mai magana da yawun kwamitin neman zaben shugaban kasarsa, Ahmed Buhari.
Anyim Pius Anyim ya nuna takaicinsa ga dinbin mutanen da su ka samu rauni da kuma wadanda aka rasa, da duk mutanen da ‘yan bindigan su ka dauke.
Shawarar Anyim Pius Anyim
A wannan jawabi, Ahmed Buhari ya kawo maganar wasikar da Anyim Pius Anyim ya aikawa Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Anyim ya ja hankalin Mai girma Buhari cewa karfin soja kadai ba zai iya kawo rashin tsaro ba, don haka ya bada shawarar yadda za a bi, a kawo zaman lafiya.
An tsaida yawon kamfe sai wani makon
‘Dan siyasar bai tsaya a ta’aziyya da Allah ya kyauta ba, ya dakatar da duk yawon kamfen da yake yi.
“Sanata Anyim ya soke duk wasu harkokin siyasar da yake yi da ziyarar neman jin ra’ayin jama’a a tsawon makon nan.”
“Saboda tunawa da wadanda aka hallaka, da kuma sauran Bayin Allah da har yanzu su ke hannun miyagun ‘yan bindiga.”
“A yayin da mu ke fatan samun sauki ga wadanda suka samu rauni, da rokon samun dangana ga wadanda suka yi rashi.”
- Kwamtin yakin Pius Anyim
An rahoto tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya bukaci ayi bincike na musamman a kan lamarin, kuma jami’an tsaro su kubutar da wadanda aka yi gaba da su.
Amaechi ya ziyarci Kaduna
A jiya aka ji Ministan sufuri na tarayya ya ziyarci inda ‘yan ta’adda su ka tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, kuma ya koka a kan karancin kayan aikin da ake bukata.
Hon. Rotimi Amaechi ya ce tun farko sai da ya bukaci a kashe N3bn wajen sayan wasu kayan tsaro, amma sai aka ki. A karshe dai hakan ya jawo an yi babbar asara.
Asali: Legit.ng