Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da Abdullahi Adamu, sabon shugaban APC
Bisa ittifakin gwamnonin da zabin shugaba Muhammadu Buhari, Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC.
An sanar da shugabancn Abdullahi Adamu ne a taron gangamin jam'iyyar dake gudana ne ranar Asabar, 26 ga Maris, 2022 a birnin tarayya Abuja.
Legit.ng Hausa ta binciko muku wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan mutumi
1. Shekarunsa 75
An haifi Sanata Abdullahi Adamu ranar 23 ga watan Yuli, shekarar 1946 a garin Keffi, yammacin jihar Nasarawa
2. Karatunsa
Ya halarci makarantar sakandaren gwamnati dake Makurdi (1960–1962), GTC Bukuru a jihar Filato (1962–1965), sannan Kaduna Polytechnic (1965–1971).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga baya a 1987 ya shiga jami'ar Jos inda yayi karatun zama lauya kuma ya kammala a 1992. Ya zama cikakken lauya a 1993.
Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC
3. Tsohon ma'aikacin Abacha ne
Bayan shiga siyasa a 1977 da kuma nasara a zaben majalisar da ta rubuta kundin tsarin mulkin Najeriya na jamhuriyya ta biyu (1978-1983).
Daga baya marigayi janar Sani Abacha ya nadashi majalisar shawara ta kasa a 1994.
A 1995, Abacha ya sake nadashi karamin ministan ayyuka da gidaje zuwa 1997
4. Daya daga cikin wadanda suka kafa PDP
Yayinda ya harkokin siyasa suka dawo a 1997, Abdullahi Adamu ya shiga jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP).
Amma bayan shekara guda suka kafa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
5. Ya yi gwamnan jihar Nasarawa tsawon shekaru 8
Dawowar demokradiyya a 1999, Abdullahi Adamu ya zama gwamnan jihar Nasarawa bayan samun nasara a zabe.
Bayan karewar wa'adinsa na farko, ya sake takara a 2003 kuma yayi nasara.
6. Shekarunsa 11 a majalisa
Bayan sauka daga gwamna a 2007 da hutun shekaru hudu, Abdullahi Adamu ya koma majalisar dokokin tarayya wakiltar mazabar Nasarawa ta yamma a majalisar dattawa a 2011.
7. Shekaru 44 a siyasa amma bai taba fadi zabe ba
Wannan babban nasara da Sanata Abdullahi Adamu ke alfahari da shi itace tun da ya shiga siyasa ba'a taba kada shi ba tun 1978.
Kwanakin baya yace:
"Daga 1978 zuwa yanzu, ban taba fadi wani zabe ba. Ni ne kusan mutumin karshe da ya bayyana niyyar takara da gangan nayi hakan."
Asali: Legit.ng