Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a

Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a

  • Kungiyar addinin Musulunci Izalah ta bude sabon ginin Masallaci a unguwar Utako dake birnin tarayya Abuja
  • Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da bude taron a matsayin babban bako
  • Shugaban kungiyar, Imam Abdullahi Bala Lau, ya yi addu'an zaman lafiya ga Najeriya kuma ya ja hankalin shugaban kasa

Utako, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron bude sabon Masallacin da kungiyar da'awa ta addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS ta gina a birnin tarayya Abuja.

An bude Masallacin ne yau Juma'a, 25 ga Maris, 2022.

Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako na musamman a taron bude Masallacin.

Daga cikin wadanda suka halarci taron bude Masallacin akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan; Ministan birnn tarayya Abuja, Muhammad Bello; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar; da Kwamishanan ilimi na biyu na jihar Kano, Alaramma Ahmed Sulaiman, dss.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Maishadda da Zukekiyar Amaryarsa Jaruma Hassana sun shilla Dubai yawon shakatawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masallacin Izalah
Da duminsa: Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a Hoto: Tope Brown
Asali: Facebook

Kalli bidiyon:

A jawabin hadimin Shugaban majalisa, Ahmad Lawan, yace:

"Da ranan nan, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya halarci Sallar Juma'a a sabon masallacin da shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Abuja Muhammad Bello da Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar, suka kaddamar."

Izalah ta gina katafaren Masallaci da kudin fatun layya a Abuja

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar JIBWIS za ta bude sabon Masallacin da ta gina a birnin tarayya Abuja ranar Juma'a.

Jibwis a jawabin da ta saki ranar Talata ta bayyana cewa an gina ne da kudaden fatun layya da mutane ke badawa fisabilillah.

Izalah ta bayyana hotunan Masalaccin dake unguwar Utako, kwaryar garin Abuja.

Yan Najeriya da suka halarci taron sun bayyana mana yadda taron ya gudana da jawaban da akayi

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da Abdullahi Adamu, sabon shugaban APC

Legit ta tuntubi wasu mambobin kungiyar Izalah da kuma Limamai a birnin tarayya Abuja don jin ra'ayinsu kan wannan gini.

Limamin Masallacin marigayi Alh Bello Damagun dake unguwar Asokoro, Sheikh Muhammadu Sani, ya bayyana cewa:

"Kamar Yadda Naji Ance Tahanyar Fatun layya Aka Gina Masallacin.
Inko Hakane Ashe Al-ummah Zasu Iya Anfanar Dakansu Dakansu Batareda Dogaro Dawani Attajiri Ko Wata Hukuma .
Sanna Alhamdulillah Ginin Masallaci Yayi Kyau kwarai Dagaske Duba da Yadda Aka Qawatashi Da Abubuwan Zamani.
Aqarshe munama Qungiyar Jibwis Nigeria Fatan Al-khairy Dacin Nasara Cikin Al-amuranta Datake Gudanarwa Naciyarda Addinin Musulunci da Musulmai Gaba."

Limamin Masallacin Efab Estate dake unguwar Lokogoma, Mal Abubakar Ibrahim Shehu, ya ce:

"An gina Masallacin ne da kudin fatun layya da Kuma gudunmuwan da wasu daidai kun mutane suka bada.
Sannan ginin masallacin yana muhimmanci idan akai la'akari da gurin da aka gina masallacin, cibiyace ta addinin musulunci, ita Kuma Islamic Center bazata cikaba saida masallacin.

Kara karanta wannan

Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

Masallaci shine guri mafi muhammanci a bayan kasa don haka duk inda aka ginashi inda za'araya shi da Ibadah to lallai abune mai kyau.
Akwai Mayan Malamai da suke karanta da al'umma a Wannan gurin."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng