'Karin bayani: Jiga-jigan sanatocin APC za su gana da shugaba Buhari a yau Alhamis
- Bayan ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC, shugaba Buhari zai gana da jiga-jigan sanatocin APC a Abuja
- Rahoton da muka samo daga majiya ya bayyana cewa, za su yi zaman ne da misalin karfe 12 na rana
- Shugaban ya gana gwamnoni a baya, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi taron gangamin APC
FCT, Abuja - Jiga-jigan jami’an majalisar dattawa da aka zaba a karkashin inuwa jam’iyyar APC a yau za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta Villa da ke Abuja.
Jaridar Daily Sun ta tattaro cewa ana sa ran sanatocin za su isa Cibiyar Taro na Gidan Gwamnati da karfe 11:30 na safe don gwajin Korona kafin daga bisani su shiga ganawa da shugaban a daidai karfe 12:30 na rana.
Shugabancin APC: Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, Gwamna ya fasa kwai
Tun dawowar shugaban kasa daga birnin Landan inda yaje jinya, shugaban ya gana da tawagar gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar APC.
A wannan karo, shugaban zai gana da sanatoci. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san dalilin ganawar tasu ba, amma ana kyautata zaton batu ne da ya shafi taron gangamin APC.
Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa kan harkokin da suka shafi yada labarai ya bayyana ganawar Buhari da shugabannin majalisar.
A cewarsa:
"Bayan ganawa da mambobin kungiyar gwamnonin APC da masu neman shugabancin jam’iyyar APC a jiya, shugaban kasa @MBuhari a yammacin yau ya yi irin wannan ganawa da shugabannin jam’iyyar APC a majalisar dokokin kasar."
Shugabancin APC: Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, Gwamna ya fasa kwai
A wani labarin, gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.
Tribune Online ta rahoto gwamnan na cewa Shugaba Buhari na goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama shugaban APC na gaba.
A ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022, APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa wanda zata zaɓi shugabanninta.
Asali: Legit.ng