Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC

Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC

  • Tun bayan sulhunta rikicin shugabancin APC, Buhari na son zama da yan takara kujerar
  • Shugaba Buhari gabanin zuwansa Landan ya zabi Abdullahi Adamu matsayin wanda yake so
  • Sauran yan takaran musamman Tanko Almakura sun ce basu yarda da zabin shugaba Buhari ba

Abuja - Domin tabbatar da ba'a samu matsala a taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Shugaba Muhammadu Buhar zai gana da yan takarar yau.

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta zabi sabbin shugabanninta na kasa ranar Asabar a farfajiyar Eagles Square dake birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun gabata cewa Shugaba Buhari na goyon bayan Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa.

Amma wasu gwamnoni da yan majalisar dattawa basu amince da Adamu ba.

Jam'iyyar APC
Gudun rikici, Shugaba Buhari zai gana da yan takarar kujerar shugaban APC
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya

Jaridar TheNation ta ce wata majiya da daren jiya tace Shugaba Buhari zai gana da yan takaran kujeran shugaban jam'iyyar domin jaddada wanda yake goyon baya ko kuma ya bada dama a fafata.

Wadanda ke neman kujerar sun hada da:

Tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu; Malam Saliu Mustapha; Sanata Sani Mohammed Musa; Mohammed Etsu; Minista George Akume da tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari.

Majiyar tace:

"Saboda tsoron abinda ka iya biyo bayan rikicin neman kujerar shugabancin APC, shugaban kasa ya gayyacesu ganawa ranar Laraba a fadar shugaban kasa."
"Ina tunanin zaman zai bada daman yin taro babu rikici. Shugaban kasa kuma zai iya tallata wadanda yake so ga yan takaran idan zasu yarda."
"Yan takaran sun ki janyewa juna, hakan na raba kan gwamnonin APC da shugabanni.

Jam'iyyun da sukayi maja a 2014 aka kafa APC sun ce basu amince Abdullahi Adamu ya zama shugaban uwar jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Legas kaddamar da ayyuka

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Shugaban kwamitin tsare-tsare na APC, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu ta mayar da hankali kan taron gangami ne, kuma ba ta da lokacin sauraran kafafen yada labarai ko kuma masu wasa da hankalinta, inji rahoton PM News.

Buni wanda ya kasance maudu'in cece-kuce a makonnin da suka gabata biyo bayan rade-radin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kore shi daga mukaminsa, ya ci gaba da cewa jam’iyyar ba za ta lamunci duk wani nau’in raba hankali a cikinta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng