‘Yan bindiga sun yi awon gaba da sabuwar Amarya, sun sha alwashin sai an biya N10m
- Kwanakin baya wasu ‘yan bindiga su ka tare fasinjoji a garin Jere da ke tsakanin Kaduna da Abuja
- Halimah Oguntoyinbo ta na cikin mutanen da suka shiga hannun ‘yan bindigan, ana neman N10m
- Wannan mata tayi aure a shekarar 2021, ta na daf da kammala digirgir, sai tsautsayi ya auka mata
Kaduna - ‘Yanuwa, surukai da iyalin wata amarya da aka yi garkuwa da ita kwanan nan sun shiga halin dar-dar yayin da aka bukaci sai an biya fansar N10m.
Rahoto ya fito daga Abusite wanda ya nuna wata Baiwar Allah mai suna Halimah Oguntoyinbo mai shekara 28 ta na cikin wadanda aka sace kwanaki a hanya.
A ranar Asabar 5 ga watan Maris 2022, miyagu suka tare matafiyan da ke shirin zuwa Legas a wata mota mai cin fasinjoji 18 a garin Jere a titin Kaduna-Abuja.
Da farko wasu mutane ne masu shigar sojoji suka tare motar, sai daga baya jama’a su ka ankara cewa ‘yan bindiga ne, don haka kowa ya nemi mafaka cikin jeji.
Sojoji sun ceci matafiya
Daga baya rundunar sojoji sun hallara wannan wuri, suka ceci matafiyan. Amma daga bisani aka fahimci cewa ‘yan bindigan sun yi nasarar dauke fasinjoji biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Halimah Oguntoyinbo wanda ‘daliba ce a jami’ar ABU Zaria ta na cikin wadanda tsautsayi ya auka masu. Bayan ita akwai wani mutumin da ba a san sunansa ba.
Shirin kammala M.Sc
Kamar yadda wata ta shaidawa The Nation, Halimah Oguntoyinbo ta na zaune a garin Legas. ‘Dalibar ta zo ABU Zaria ne domin gabatar da kundin digirinta.
Wata majiyar ta bayyana cewa Oguntoyinbo ta na karatun digirgir ne a wannan jami’a a Zaria. ‘Dalibar tayi digirin farko ne a ilmin ma’adanai kafin tayi aure.
Oguntoyinbo sun tattara sun koma Ogun bayan mahaifinsu ya rasu. A Nuwamban shekarar 2021 wannan mata tayi aure inda ta ke zaune da mai gidanta a Legas.
An sa kudin fansar Halima
A ranar 9 ga watan nan ‘yan bindigan suka tuntubi ‘yanuwanta, suka bukaci a biya fansar N100m. Daga baya aka ji miyagun sun rage wannan kudin zuwa N10m.
‘Yanuwanta ba za su iya biyan wannan kudi ba domin ba su da hali. Mahaifinta ya yi ritaya kafin ya rasu, miijin na ta kuma bai da halin biyan wadannan miliyoyi.
An sace Farfesa a Edo
Duk a makon nan, labari ya zo cewa miyagun ‘Yan bindiga sun dauke wani malamin jami'ar Ambrose Ali da ke Ekpoma a hanyar Ubiaja-Ewohimi a jihar Edo.
Farfesa M. A. Izibili yana cikin wasu fasinjojin da aka yi garkuwa da su a karshen makon da ya wuce. Abin ya faru ne yayin da ya ke dawowa daga daurin aure.
Asali: Legit.ng