Matsalar tsaro ta fatattaki Bayin Allah 700, 000 daga gidajensu a Zamfara inji Kwamishina
- Gwamatin Zamfara ta na dawainiya da mutane fiye da 700, 000 da matsalar rashin tsaro ta shafe su
- Ibrahim Magaji Dosara wanda shi ne Kwamishinan yada labaran Zamfara ne ya bayyana wannan
- Kwamishinan tsaro ya ce gwamnatin Muhammad Bello Matawalle ta dauki ‘yan banga har 4200 aiki
Kaduna - gwamnatin jihar Zamfara ta ce ma’aikatar bada agaji ta kafa cibiyoyi takwas domin kula da wadanda su ke sansanin gudun hijira a garuruwan jihar.
Daily Trust ta rahoto gwamnatin ta na cewa akwai sama da mutane 700, 000 da ke gudun hijira.
Kwamishinan yada labarai na Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa gwamnati na dawainiya da masu gudun hijira.
Alhaji Ibrahim Magaji Dosara ya ce a kowace karamar hukuma da ke jihar Zamfara, akwai jami’an bada agaji na gaggawa da aka samar domin su bada taimako.
Wadannan jami’ai za su rika bada tallafi ga wadanda matsalar tsaro ta shafa a kowace karamar hukuma.Akwai kananan hukumomi 14 ne a jihar ta Zamfara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Baya ga rabon kayan abinci, katifa, gado, tufafi da sauransu da gwamnatin jiha ta ke yi, ma’aikatar ta na yabon kokarin da kungiyoyin kasashen waje ke yi.”
“Wadannan kungiyoyi su na karfafawa gwamnatin jihar ta hanyar bada kudi ga masu gudun hijira, ana raba N30000 zuwa N40000 ga wadanda abin ya shafa.”
“Gwamnatin tarayya ta narka makudan kudi a kan haka Gwamnatin Zamfara ta na godewa duk wadanda suka taimaka wajen yaye wa mutanenta bakin ciki.”
- Alhaji Ibrahim Magaji Dosara
An rahoto kwamishinan yana cewa ana horas da wadanda ‘yan bindiga suka fatattaka. Ana koya masu tukin keke napep, tela, hada ruwa, wanzaci da sauransu.
An dauki 'yan sa-kai
Kwamishinan tsaro da harkokin gida, Mamman Ibrahim Tsafe ya ce sun dauki ma’aikatan sa-kai 4200 aikin banga domin su kare jama’a daga ta'adin ‘yan bindiga.
DIG Mamman Tsafe ya ce an koyawa ma’aikatan rike makami domin su taimakawa jamii’an tsaro.
Buhari ya zauna da Uzodinma
Biyo bayan tashin hankalin da aka samu a jihar Imo, lambar Gwamna Hope Uzodinma ta fito a fadar Shugaban kasa, inda ya sa labule da shugaba Buhari.
Ana da labarin cewa matsalar wutar lantarki ta jawo Muhammadu Buhari yi zama naya musamman da Ministansa daga dawowa bakin-aiki a jiya.
Asali: Legit.ng