Yayin da ASUU ta ke yajin-aiki, an yi garkuwa da wani Farfesa daga zuwa daurin aure
- Miyagun ‘Yan bindiga sun dauke wani malamin makaranta a hanyar Ubiaja-Ewohimi a jihar Edo
- Farfesa M. A. Izibili yana cikin wasu fasinjojin da aka yi garkuwa da su a karshen makon da ya wuce
- Izibili malamin falsafa ne a jami’ar Ambrose Alli da ya fadawa tsautsayi daga zuwa daurin aure
Edo - Wani labari mara dadi yana zuwa mana inda aka ji cewa miyagun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Farfesa M. A. Izibili a Ubiaja, garin Easan, jihar Edo.
Daily Trust ta ce Farfesa M. A. Izibili malami ne a jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma, jihar Edo.
M. A. Izibili ya fada hannun ‘yan bindiga ne yayin da yake dawowa daga wajen wani daurin aure da aka yi a garin Uromi duk a jihar Edo tare da wasu matafiyan.
Miyagu sun fito daga cikin jeji sun tare matafiya a kan titin Ubiaja zuwa Ewatto. A nan aka tilasta motarsu ta tsaya, sannan aka shiga da su cikin kungurmin jeji.
Wata majiya daga jaridar Independent ta ce da farko har da mai dakin wannan shehin malami aka kama. Daga baya aka sake ta domin ta iya ba mutane labari.
‘Yan bindigan su na neman a biya Naira miliyan 10 idan ana so wadannan Bayin Allah su kubuta.
Shugaban kungiyar ASUU na reshen jami’ar Ambrose Alli, Cyril Onogbosele ya tabbatarwa manema labarai cewa babu shakka an yi garkuwa da malaminsu.
Onogbosele ya ce an sace Farfesan ne tsakanin Ubiaja da Ewohimi, yana kan hanyar dawowa garin Ekpoma. Izibili ya na koyar da ilmin falsafa ne a makarantar.
Haka aka yi - 'Yan Sanda
Jaridar ta ce Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Edo, SP Kontongs Bello ya tabbatar da aukuwar wannan mumunan labari.
SP Kontongs Bello ya ce jami’an tsaro na kokarin ceto wadannan mutane ba tare da ko kwarzane ba.
Daga jin labarin abin da ya auku, ‘yan banga su ka karada dajin amma babu labarin inda su ke har zuwa yanzu. Ba mu da masaniya game da kudin fansar da ake nema.
An kashe 'Yar APC a jeji
Idan za ku tuna, kwanakin baya ne ‘Yan bindiga suka yi garkuwa da wasu shugabannin jam’iyyar APC a Kwara su na hanyar dawowa daga taro a gidan gwamn a Ilorin.
Daga ciki har da wasu jagorori na mata na APC wanda yanzu haka Olomi Sunday ta rasu yayin da ake musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da kuma wasu 'yan banga.
Asali: Legit.ng