Jerin tsofaffin gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta damƙe bayan tube musu rigar kariya

Jerin tsofaffin gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta damƙe bayan tube musu rigar kariya

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama gwamnonin Najeriya da dama bayan tube musu rigar kariya
  • A binciken da muka tattara hukumar ta yi ram da aƙalla tsofaffin gwamnoni 33 bisa tuhume-tuhume da suka shafi halasta kuɗin haram
  • Na baya-bayan nan shi ne gwamnan jihar Anambra, wanda EFCC ta kama shi awanni kadan bayan miƙa mulki

Abuja -Tun bayan dawowar mulkin Demokaraɗiyya a jamhuriya ta haɗu 1999 zuwa yanzun, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta yi ram da gwamnoni 33 a Najeriya bayan sauka daga mulki.

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, shi ne na baya-bayan nan da hukumar ta kama awanni bayan miƙa mulki, kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi

A mafi yawan lokaci, hukumar dake yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta'asa tana tuhumar gwamnonin da karkatar da kudin al'umma ko na ayyuka zuwa aljihunansu.

Sai dai kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa matuƙar gwamna na kan mulki, babu mai tuhumarsu saboda rigar kariya.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin tsofaffin gwamnoni 33 da suka shiga hannun EFCC bayan sauka daga kan karagar mulki.

1. Willie Obiano

Gwamna Obiano
Jerin tsofaffin gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta damƙe bayan tube musu rigar kariya Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano, ya shiga hannun hukumar EFCC a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, 20222.

EFCC ta kama shi awanni kaɗan bayan mika mulki kuma ta ce ta jima tana bibiyarsa amma saboda rigar kariya ta jira har wannan lokacin.

2. James Ibori

Bayan sauka daga mulki, James Ibori, wanda ya shafe shekara 8 a matsayin gwamnan jihar Delta daga 1999-2007 ya tsere daga Najeriya tun kafin a kama shi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC

A shekarar 2010 ya shiga hannu a Dubai, daga nan aka zarce da shi Burtaniya inda ya fuskanci hukuncin Kotu na zaman gidan Yari tsawon shekara 13.

A gaban Kotun, tsohon gwamnan ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da suka haɗa da almundahana da karkatar da kuɗaɗe.

3. Bukola Saraki

Tsohon gwamnan jihar Kwara, Abubakar Bukola Saraki, ya sha fama da binciken EFCC lokacin yana kan kujerar shugaban majalisar dattawa.

A matsayinsa na mutum lamba na uku a Najeriya, EFCC ta tuhumi Saraki da kin bayyana gaskiyar yawan kadarori da dukiyarsa.

Bukola Saraki
Jerin tsofaffin gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta damƙe bayan tube musu rigar kariya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A shekarar 2018, Kotun ƙoli ta wanke Saraki, amma EFCC ta sake kama shi bisa tuhume-tuhumen sama da faɗi da kuɗaɗen kasa da halasta na haram.

Sauran gwamnonin sune kamar haka:-

4. Rochas Okorocha (Imo)

5. Orji Uzo Kanu (Abia)

6. Peter Ayodele Fayose (Ekiti)

7. Gabriel Suswam (Benuwai)

8. Audu Abubakar (Kogi)

9. Abdullahi Adamu (Nasarawa)

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance

10. Aliyu Akwe Doma (Nasarawa)

11. Joshua Dariye (Filato)

12. Jonah Jang (Filato)

13. James Bala Ngilari (Adamawa)

14. Murtala Nyako (Adamawa)

15. Ali Modu Sheriff (Borno)

16. Danjuma Goje (Gombe)

17. Jolly Nyame (Taraba)

18. Sule Lamido (Jigawa)

19. Aliyu Wammako (Sokoto)

20. Abdulaziz Yari (Zamfara)

21. Theodore Orji (Abia)

22. Chimaroke Nnamani (Enugu)

23. Sullivan Chime (Enugu)

24. Ikedi Ohakim (Imo)

26. Godswill Akpabi (Akwa Ibom)

27. Diepreye Alamieyeseigha (Bayelsa)

28. Timipre Sylva (Bayelsa)

29. Lucky Igbinedion (Edo)

30. Olugbenga Daniel (Ogun)

31. Adebayo Alao-Akala (Oyo)

32. Rashidi Ladoja (Oyo)

33. Muktar Ramalan Yero (Kaduna)

A wani labarin kuma 'Zan cika burin yan Najeriya' Matashi dan shekara 45 ya shiga tseren gaje kujerar Buhari a 2023

Matashi ɗan shekara 45 daga jihar Osun yace lokaci ya yi matasa zasu fito su karbi ragamar mulkin Najeriya.

Mista Joseph, wanda ya bayyana shiga tseren takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya a 2023, ya ce ya shirya tsaf domin kawo canji.

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262