Fuskar Ma’aikaciyar bankin da hukumar EFCC ta kama da almundahanar N450m

Fuskar Ma’aikaciyar bankin da hukumar EFCC ta kama da almundahanar N450m

  • Hukumar EFCC ta cika hannu da ma'aikaciyar bankin da ta karbi kudin cin hanci hannun kwastamomi
  • EFCC ta gurfanar da matar gaban kuliya inda ta musanta zargin da ake yi mata
  • Bankin da take wa aiki United Bank for Africa, UBA suka kai kararta wajen hukumar ta EFCC

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta gurfanar da wata mata ma’aikaciyar bankin da ta wawuri miliyoyin kudi.

Matar mai suna Judith Nnewka Nnagwu ta kasance Ma’aikaciyar bankin, reshen jihar Anambra.

A jawabin da EFCC ta saki, Judith ta karbi naira miliyan dari da casaín da biyu da naira miliyan dari biyu da sittin da dubu arbaín da bakwai.

Fuskar ma’akaciyar bankin da hukumar EFCC ta kama da almundahanar N450m
Fuskar ma’akaciyar bankin da hukumar EFCC ta kama da almundahanar N450m
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi

Ga jawabin EFCC:

“Hukumar EFCC reshen Enugu ranar Laraba, 16 ga watan Maris, 2022, ta gurfanar da Hukumar, wata ma’aikaciyar bankin United Bank for Africa, UBA, a gaban mai shari’a D.A Onyefulu na babar kotun jihar Anambra dake zama a Onitsha akan tuhuma bakwai mai alaka da samar da takardun bogi da karya da zamba ta nera miliyan dari hudu da hamsin da biyu da dubu arbaín da bakwai
EFCC na zargin Judith da karban nera miliyan dari da casaín da biyu a wajen wanda ya kawo korafin wanda take kula mata da asusunta na banki da cewa bankin na da dala dubu dari hudu da zai sayar akan nera dari hudu da tamanin.
Bankin UBA ma ya kawo korafinsa ga hukumar EFCC inda ya bayyana cewa ta karbi kudi nera miliyan dari biyu da sittin da dubu arbaín da bakwai a wurin wani mai hulda da banki.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

Ta musanta laifin da ake tuhumar ta da shi.
Mai shari’a Onyefulu ya bayar da belinta akan nera miliyan goma da wani mai tsaya mata inda yadaga sauraren karar zuwa 11 ga watana Mayu, 2022.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng