Gobara ta kona wurin da hukumar EFCC ta ke tara hujjar binciken marasa gaskiya

Gobara ta kona wurin da hukumar EFCC ta ke tara hujjar binciken marasa gaskiya

  • Hukumar EFCC ta ce wuta ya kama a wata bola da ta ke tattara hujjojin binciken da ta ke yi
  • Mr. Wilson Uwujaren ya fitar da jawabi yana cewa abin ya auku ne a Iriebi da ke jihar Ribas
  • Sakataren hukumar EFCC, George Ekpungu ya na Fatakwal domin binciken abin da ya faru

Rivers - Wuta ta barke a wata bola da hukumar EFCC ta ke ajiye hujjoji da bayanan binciken da ta ke yi a kan wadanda ake zargi da rashin gaskiya.

Punch ta kawo rahoto a ranar Laraba, 16 ga watan Maris 2022 cewa wanan wuri da ake tara hujjoji yana nan ne a garin Iriebi, a Fatakwal, jihar Ribas.

Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC na kasa, Wilson Uwujaren ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar a Abuja a yammacin ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6

Wilson Uwujaren ya ce gobarar ta shafi wasu manyan motocin da aka ajiye ne a garin Iriebi.

The Cable ta ce Uwujaren ya bayyana cewa babban jami’in hukumar EFCC, George Ekpungu ya kai ziyara zuwa wurin domin binciken abin da ya faru.

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta tabbatar da cewa ana ta bincike da nufin kawo karshen faruwar irin haka a gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar EFCC
Hedikwatar EFCC Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Jawabin kakakin hukuma

“An samu gobara ta kama a wajen ajiye bolar hukumar EFCC da yake yankin Iriebi, garin Fatakwal, a jihar Ribas.”
“Wutar ta kama ne a ranar Litinin, 14 ga watan Maris 2022.”
“Abin ya fara ne da safiyar wannan rana, ya shafi mafi yawan motocin da aka ajiye a wurin kafin ma’aikatan kwana-kwana su kashe ta.”
“Sakataren hukumar, Dr. George Ekpungu wanda ya zo wurin da abin ya faru a ranar Talata, 15 ga watan Maris ya tabbatar da cewa an soma bincike domin gano asalin abin da ya jawo gobarar.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna

“Sannan ana daukar mataki domin tabbatar an tsare duk sauran bololin ajiye hujjojin da ke fadin kasar nan.”

- Wilson Uwujaren

Wahalar man fetur

A makon nan ne mu ka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a hukunta duk wadanda suka jawo wahalar man fetur a fadin Najeriya.

Shigo da man fetur mai kunshe da tulin sinadarin Methanol ya taimaka wajen kawo wahalar mai. Har yanzu abubuwa ba su dawo daidai a jihohin kasar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng