An yaye tubabbun yan ta'addan Boko Haram 559 da aka yiwa horo
Sama da tubabbun yan Boko Haram 559 aka yaye daga shirin horaswa da sauya tunani a sansanin gyara halaye dake Mallam Sidi, karamar hukumar Kwami dake jihar Gombe.
Tsaffin yan ta'addan da aka yaye karshen makon da ya gabata sun amince da yafuwar gwamnati kuma sun ajiye makamansu.
Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Adeyemi Yekini ya shawarci tubabbun yan ta'addan su kasance masu bin doka, rahoton ChannelsTV.
Ya bayyana cewa an horas da tsaffin ta'addan wajen aikin tela, hada takalmi, hada hula, kafinta, wanki da guga, kuma ana kyautata zaton zasu iya taimakon kansu da iyalansu.
Kwamandan Operation Safe Corridor, Joseph Maina, wanda yayi jawabi a taron ya bayyana cewa a shekarar 2015 Shugaba Buhari ya kafa shirin wayar da kai da sauya tunanin tubabbun yan ta'addan Boko Haram.
Yace:
"Tun da aka fara shirin ne, an yaye tsaffin yan ta'adda 1070 kuma an mayar da su cikin al'umma. Yau kuma, wasu mutum 559 za'a yaye daga shirin kuma su koma cikin al'ummarsu."
"Gaba daya an duba lafiyar wadannan mutum 559, an koya musu illolin kwaya, an koyar dasu ilmin Boko da na addini."
A taron, an bukaci tsaffin yan ta'addan su rantse da Al-Qurani na cewa angulu ba zata koma ruwa ba.
Kalli bidiyon:
Asali: Legit.ng