Tattalin arziki: Najeriya na fuskantar barazanar asarar sama da Naira Biliyan 1 a kullum

Tattalin arziki: Najeriya na fuskantar barazanar asarar sama da Naira Biliyan 1 a kullum

  • Fashewar kayan aiki a karamar hukumar Nemben jihar Bayelsa ya kawowa gwamnatin tarayya cikas
  • Hakan ya kawo kamfanin Nigerian Agip Oil Company sun daina fita da danyen mai zuwa kasashen waje
  • Wannan ya yi sanadiyyar da Najeriya za ta rasa fiye da Naira biliyan 1 da ya dace ta samu daga mai kullum

Bayelsa - Matsalar tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta ta kama wata hanyar bayan Agip ya bada sanarwar dakatar da aiki a sashen jihar Bayelsa.

Jaridar Daily Trust ta ce kamfanin na Agip ya tsaida hako ganguna 25, 000 na danyen mai da yake yi a yankin Brass a sakamakon hadarin da suka samu.

Kamfanin Nigerian Agip Oil Company (NAOC) ya fitar da sanarwa cewa an fasa wani layin mansu da ke garin Nembe, don haka suka samu matsala a aiki.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Hakan ya kuma yi sanadiyyar datse gas da ake kai wa tashar Okpai daga yankin Bonny a Bayelsa.

Hadarin da ya yi sanadiyyar fashewar kayan aiki a Neja Deltan zai iya jawowa gwamnatin tarayya rasa Dala miliyan 2.84 da ta ke samu daga danyen mai.

A duk rana ana samun kusan Naira biliyan 1.2 idan Agip ya fita da gangunan danyen mai 25, 000. Da mai ne Najeriya ta ke samun mafi yawan kudin shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tattalin arziki
Wajen hako danyen mai Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

An gaza cika sharudan OPEC

Najeriya ta dade ta na fama da tsageru a wannan bangare da suke fasa bututun danyen mai. Hakan na jawo asarar dukiya, rayuka, da rashin kudin shiga.

A sakamakon danyen aikin da tsageru suke yi a Neja-Delta, Najeriya ta gagara samar da adadin gangunan danyen man da kungiyar OPEC ta yankewa kowa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Rahoton ya ce a dalilin haka, gwamnatin tarayya ta na asarar makudan daloli a kasuwar Duniya, musamman a halin yanzu da danyen mai ya yi masifar tsada.

N1.2bn su na bin iska a kullum

Rahotanni sun tabbatar da cewa abin da aka saida gangar danyen man Bonny Light a farkon makon nan ya kai akalla Dala 113.6 (kusan N50, 000 kenan).

Idan aka yi lissafi, a kowace rana Najeriya za ta rasa Dala miliyan 2.84m. Kamfanin na NAOC ba zai dauki wata asara ba saboda abin da ya faru ya fi karfinsu.

Yakin Rasha da Ukraine

An ji cewa manoma su na kokawa kan yadda buhun takin zamani ya yi matukar tsada a kasuwa. Idan har farashin taki bai sauka ba, kayan abinci za su kara tsada.

Yakin Rasha v Ukraine yana cikin abubuwan da za su taimaka wajen kawo matsalar. Ukraine ta na noman abinci sosai, kuma ta na samar da sinadaran hada taki. R

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng