Abu ya lalace: NDLEA sun yi ram da Fasto a filin jirgi da kayan maye zai je ‘aikin addini’
- Jami’an NDLEA sun yi nasarar kama Ugochukwu Emmanuel Ekwem dauke da kayan shaye-shaye
- An cafke Rabaren Ugochukwu Emmanuel Ekwem ne a filin tashin jirgin saman MMIA da ke garin Legas
- Wannan Fasto ya boye wiwi a jikinsa, ya na shirin fita da su zuwa Kenya inda zai yi wani taron addini
Lagos - Babban limamin cocin Christ Living Hope Church, Rabaren Ugochukwu Emmanuel Ekwem yana hannun hukuma bisa zargin safarar kwayoyi.
Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto, mai magana da yawun bakin hukumar NDLEA a Najeriya, Femi Babafemi ya shaidawa manema labarai haka.
An kama Faston ne a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA), da ke garin Ikeja, jihar Legas.
Femi Babafemi ya ce jikin Rabaren Ugochukwu Ekwem zagaye yake da sanduna 54 na miyagun kwayoyi a jikinsa, yana shirin barin Najeriya zuwa kasar Kenya.
Fasto da tabar wiwi
Jaridar ta ce da aka yi gwaji, sai aka gano wannan malamin addini yana dauke ne da wiwi. Ekwem ya amsa laifinsa da jami’an NDLEA suka taso shi a gaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin da hukumar ta fitar ya bayyana cewa an kama Faston ne tun a ranar 7 ga watan Maris 2022, ana kokarin tantance masu shiga jirgin Ethiopian Airlines.
Jawabin Femi Babafemi
“Da aka yi bincike, sai aka gano sandunan da yake dauke da su na tabar wiwi ne. Malamin ya tabbatar da laifinsa a lokacin da aka yi magana da shi.”
“Ya ce zai yi amfani da wadannan miyagun kwayoyin da suke jikinsa ne a makonni ukun da zai yi wajen taron addini a kasar Kenya.” – Femi Babafemi.
The Nation ta ce cocin da matashin yake jagoranci yana kan titin Isuaniocha, Mgbakwu ne a Awa, jihar Anamabra, yana kuma da wasu coci biyu a Legas da Abuja.
A daidai wannan rana ne kuma aka kama wani fasinja, Nnakeanyi Chukwuka King wanda ya dawo Najeriya daga kasar Brazil dauke da sinki 40 na hodar iblis.
Da jami’ai suka yi bincike, sai suka gane cewa Nnakeanyi Chukwuka King yana dauke da kilogram na 9.7 na kwayar a boye cikin wasu robobin man shafawa.
Bayan nan an samu kwalaben 1807 codeine a Kaduna da kwayoyi wajen wani matashi a Anambra.
Coci sun shiga siyasa?
A karshen makon jiya ne aka ji shugabannin cocin Redeemed Christian Church of God sun bada umarni a kafa bangarorin siyasa a kowane cocinsu da ke kasar nan.
Ana tunanin wadannan sassa na siyasa da shugabanci da za a kafa za su taimakawa Farfesa Osinbajo idan har mataimakin shugaban Najeriyan zai tsaya takara.
Asali: Legit.ng