Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

  • A makon da ya gabata, yan ta'adda sun zafafa kai hare-hare kan jami'an tsaro da yan kasa nusamman a arewacin Najeriya
  • Mun tattaro muku yadda aka kashe aƙalla mutum 103 a faɗin Najeriya cikin mako guda, wanda ya haɗa za jami'an tsaro 24
  • A wannan mako ne yan bindiga suka farmaki tawagar mataimakin gwamnan jihar Kebbi

Akalla mutum 103 ne suka rasa rayukansu a hannun yan ta'adda a Najeriya cikin makon da ya gabata (6 ga watan Maris zuwa 12 ga watan Maris), kamar yadda Premium Times ta tattaro.

Rasa rayukan da aka samu a makon da ya gabata ya nuna alamun samun karuwar kashe mutane da kashi 900% idan aka kwatanta da na makon da ya shuɗe kafin shi.

Haka nan kuma alƙaluman mutanen da suka rasa rayukan su a wancan makon na baya shi ne ma fi ƙaranci tun bayan shigowar shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An kuma sace kananan yara yan shekara 4 a Keke Napep bayan tashi daga makaranta

Daga cikin mutum 103 da aka kashe, 24 jami'an tsaro ne da suka haɗa da sojoji 18, da yan sanda shida, yayin da sauran 76 duk fararen hula ne da basu ji ba kuma ba su gani ba.

Yan bindiga
Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mafi yawan kashe-kashen sun auku ne a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya, yayin da kalilan aka samu a wasu tsirarun jihohi.

Ba'a samu rahoton matsala a jihohin Zamfara, Sokoto da Neja ba, waɗan da babu tantamar cewa suna daga cikin jihohin da lamarin rashin tsaro ya fi wa illa.

Jaridar Premium Times ta tattara waɗan nan alkaluman ne daga labaran da kafafen watsa labarai suka ruwaito, babu adadin wanda ba'a rahoto ba.

Ga jerin yadda lamarin ya auku daki-daki:

Mutum biyu a Kaduna

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Yan bindiga sun halaka mutum biyu kuma suka yi awon gaba da malamin Cocin Katolika, Joseph Akeke, a ƙauyen Kidendan dake jihar Kaduna.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya auku da ƙarfe 1:00 na daren ranar Talata lokacin da yan bindigan suka farmaki ƙauyen.

Mutum 82 a jihar Kebbi

Aƙalla Yan Bijilanti 63 aka tabbatar Allah ya musu rasuwa yayin da yan bindiga suka musu kwantan ɓauna ranar Lahadi da yamma.

Sarakunan yankuna biyu da lamarin ya shafa sun shaida wa BBC Hausa cewa Yan Bijilantin sun faɗa tarkon yan bindiga ne yayin da suka bibiyi yan ta'addan da suka hana yankunan zaman lafiya.

Sai dai wasu majiyoyi biyu na sarakuna sun tabbatar wa manema labarai cewa adadin yan bijilanti da aka kashe ya zarce 63.

Kwana biyu bayan haka, yan ta'adda suka halaka sojoji 18 da yan sanda 6 yayin da suka farmaki tawagar mataimakin gwamnan Kebbi, Sama'ila Yombe, a kauyen Kanya, ƙaramar hukumar Dangu Wasagu a jihar.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan yan sanda sun kama yan bindiga 200, yan fashi 20 a jihar Kaduna

Lamarin ya faru ne lokacin da mataimakin gwamnan ya kai ziyarar jaje ga yankunan da ayyukan ta'addancin yan bindiga ya shafa.

Mutum 12 a Katsina

Ƙananan yara Bakwai suka rasa rayukan su yayin turereniyar mutane domin tserewa daga harin yan bindiga a Shimfida, karamar hukumar Jibia.

Lamarin ya faru ranar Alhamis da safe, awanni kaɗan bayan Sojojin dake aikin tsaro a yankin sun fice, a cewar mazauna Shinfiɗa.

Haka nan kuma, Fasinjoji biyar suka mutu wasu uku suka samu raunuka yayin da yan bindiga suka buɗe wa motoci wuta a hanyar Yan Tumaki – Danmusa.

Mutum ɗaya a Ogun

Wasu makasa da ba'a san ko su waye ba sun banka wa Basaraken Olowe Gbagura, wuta a ƙaramar hukumar Abeokuta ta arewa, Akin Muheedeen.

Rahotanni sun nuna cewa Basaraken ƙauyen na kan hanyar dawowarsa daga masallaci sallar Asuba ne ya gamu da makasan da suka cinna masa wuta.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

Wasu tsagerun yan bindiga sun tare hadimin gwamnan Taraba , Honorabul Gbashi, sun bindige shi har Lahira.

Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262