Za a kafa bangarorin siyasa na musamman a duk reshen cocin da Osinbajo yake aikin Fasto

Za a kafa bangarorin siyasa na musamman a duk reshen cocin da Osinbajo yake aikin Fasto

  • Shugabannin cocin Redeemed Christian Church of God sun bada umarni a kafa bangarorin siyasa
  • Ana tunanin wadannan sassa na siyasa da shugabanci da za a kafa za su taimakawa Yemi Osinbajo
  • Har zuwa yanzu Farfesa Yemi Osinbajo bai bayyana niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba

Shahararren cocin nan na Redeemed Christian Church of God wanda ake kira RCCG, zai kafa sashen siyasa da shugabanci yayin da ake shirin zabe.

Premium Times ta ce wannan cocin mai dinbin mabiya da majami’ai sama da 32, 000 a Najeriya za su marawa mabiyansu baya idan su ka tsaya takara.

A wata takarda da ta fito a watan Fubrairun 2022, an umarci dukkan fastoci da su kafa wannan sashe da zai taimakawa na su da za su shiga harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Kwadayin 2023, Jonathan, FFK da abubuwa 5 da suka jawowa Buni matsala a tafiyar APC

Babban jami’in gudanarwa na cocin, J.F Odesola ya bukaci fastoci da jagororinsu su samar da ofisoshi na wannan aiki nan da mako biyu a kowane yanki.

Rahoton ya ce Timothy Olaniyan shi ne zai jagoranci wannan bangare na musamman da za a kafa.

Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo SAN Hoto: www.yemiosinbajo.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Osinbajo za a yi wa yaki?

Jaridar People’s Gazette ta na ganin cewa an kawo wannan tsari ne domin taimakawa Yemi Osinbajo ya zama shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa.

Kafin 2015, Farfesa Osinbajo yana cikin fastocin da suke aiki da cocin RCCG. Daga nan ne aka dauko shi ya zama mataimakin Muhammadu Buhari a APC.

Ba daidai ba ne – Farfesa Kperogi

A wani tsokaci da ya yi a shafinsa, babban malamin lugga kuma mai sukar gwamnati, Farfesa Farouk Kperogi ya ce shigar coci cikin harkar siyasa bai dace ba.

Kara karanta wannan

2023: Wani Farfesan Najeriya Ya Yunƙuro, Zai Nemi Kujerar Buhari a Ƙarkshin Jam'iyyar APC

Farouk Kperogi ya ce tun farko zargin kaushin addinin Islama ya jawo Buhari ya dauko Fasto Osinbajo, hakan kuma ta sa ya jawo Fasto Tunde Bakare a 2015.

A ra’ayin malamin jami’ar, Osinbajo ya zagaye kan shi da ‘yan cocin RCCG a gwamnati ne kurum, kuma ya gagara fahimtar dabi’u da irin al’adun musulman Arewa.

Tsohon ‘dan jaridar ya ce idan kiristoci sun jefa kansu tsamo-tsamo a siyasa, musulmai za su iya yin koyi da su, wanda ya ce hakan ba zai kawo zaman lafiya ba.

Osinbajo su hakura da takara - DOJ

Shugaban kungiyar The Disciples of Jagaban ya fito yana rokon ‘Yan PDP, APC, matasa, sarakuna da sauran 'yan siyasa, su hakura su goyi bayan Bola Tinubu a 2023.

Shugaban DOJ, Abdulhakeem Alawuje yana ganin babu wanda ya cancanta da mulki irin Tinubu don haka ya kamata su Yemi Osinbajo su sallama masa a zaben.

Kara karanta wannan

Osinbajo @65: Fadar Shugaban kasa tayi magana a kan 'takarar' Osinbajo a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng