Bidiyon kyawawan tagwaye mata da suka sha alwashin auren miji daya, sun ce ba su iya rabuwa
- Belinda da Linda tagwaye ne a kasar Ghana masu matukar kama da juna da suka yanke hukuncin rayuwa tare da juna
- Tagwayen 'yan matan sun bayyana cewa basu taba rabuwa da juna ba kuma suna da buri iri daya a rayuwa
- Belinda wacce ta girma Linda da mintuna 5 ta kwatanta kanta da mai son jama'a yayin da Linda take da kame kai amma sai hatsarin gaske
Kyawawan tagwayen 'yan mata na kasar Ghana masu suna Linda da Belinda sun birge jama'a ganin irin tsananin kama da suke yi da juna a wata tattaunawa da Vibes In5 da Arnold da suka yi.
Kyawawan tagwayen sun sanar da cewa komai tare suke yi tunda aka haife su kuma suna shirin yadda za su cigaba da rayuwa a hakan ko da kuwa a harkar aure ne sai su nemi miji daya.
Belinda da Linda sun ce a rayuwarsu suna da burika da fara daya. Sun ce suna fadawa kogin soyayyar saurayi daya a lokuta da yawa.
Yayin tattaunawa da Arnold, sun bayyana cewa suna da burin zama masu gabatarwa a gidan talabijin a nan gaba ganin cewa karatu iri daya suka yi a makaranta.
Kyawawan tagwayen wadanda suka bayyana a wani shirin talabijin mai suna 'Efieruwa' sun ce suna son saurayin juna don haka suka yanke hukuncin auren mutum daya a nan gaba.
"Ba sau daya ko biyu ba, mu kan fada soyayyar saurayin juna, hakan yasa muka yanke shawarar auren namiji daya don kada mu rabu," tagwayen suka ce.
Belinda wacce ta girma Linda da minti biyar, ta kwatanta kanta da mai son shiga jama'a yayin da abokiyar tagwaitakar ta ta kasance mara son hayaniya amma mai matukar hatsarin gaske.
Aure ya yi albarka: Hotunan magidancin da ya auri mata 2 a rana guda yayin da suke murnar cika shekara 1
A wani labari na daban, masu iya magana kan ce sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a kaiba. Tafiya dai ta fara mika tsakanin wani magidanci da ya auri mata biyu a rana daya.
A bara ne dai labarin mutumin mai suna Babangida Adamu Sadiq, ya karade shafukan soshiyal midiya sakamakon auren mata biyu, Maimuna Mahmud da Maryam Muhammad Na'ibi da ya yi a rana daya.
A ranar 6 ga watan Maris din 2021 ne dai aka daura auren masoyan. Don a haka ya shirya bikin murnar zagayowar wannan rana a jiya Lahadi.
Asali: Legit.ng