Magana ta dawo baya: Gwamnati ta ce babu kudin da malaman jami'a masu yajin-aiki ke nema
- Ministan kwadago da ayyuka na tarayya ya bayyana cewa ba su da kudin da ASUU ta ke nema
- Sanata Chris Ngige ya fadawa manema labarai cewa a halin yanzu ba su da wadannan biliyoyin
- Ngige ya ce inda babbar matsalar ta ke shi ne a game da kudin farfado da jami’o’in gwamnatin tarayya
Abuja - Ministan kwadago da ayyukan yi na kasa, Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da kudin da 'yan kungiyar ASUU su ke bukata.
The Cable ta rahoto Ministan yana cewa babu isassun kudin da gwamnatin Muhammadu Buhari za ta biya bukatun da malaman jami’a suke nema a hannunsu.
Ministan ya bayyana wannan a lokacin da ya bayyana a wata tattaunawa a shirin siyasa na Politics Today a gidan talabijin Channels TV a ranar Alhamis.
Da aka tambayi Sanata Chris Ngige ko gwamnatin tarayya ta gaza cika jeringiyar alkawuran da ta yi wa malaman da suke yajin-aiki, sai Ministan ya ce a’a.
“Mu na fatan ASUU za ta yi abin da ya kamata, ta tuntubi ‘ya ‘yanta a kan zaman sasantawar da muka yi a makonni biyun da suka wuce.”
“A game da zancen alawus din EAA, mun amince za a koma ga lokacin da NUC ta tsaida na lokacin da za a biya kudin shekarar 2021.”
“A kan kudin farfado da jami’o’in gwamnati, babu tabbacin ko nawa aka biya.” - Chris Ngige.
Babu kudi a kasa
Daga cikin N1.3tr da ya kamata a biya tsakanin 2013 da 2018, abin da jami’o’i suka samu a 2013 bai wuce N200bn, sai kuma N70bn a cikin shekaru bakwai.
“Gwamnati ta na cewa a yanzu ‘ba mu da wadannan kudin da za mu biya.’ Wannan yarjejeniyar da aka yi a 2016 da 2017 kenan.” – Chris Ngige.
A cewar Ministan, idan dai ba yaudara za ayi ba, a biya jami’o’i daga cikin kason hukumar TETFund ba, babu ta inda wadannan biliyoyin za su iya fitowa.
Yajin-aiki ya kusa zuwa karshe
Kwanaki aka ji cewa Dr. Chris Ngige ya fadi inda aka kwana a tattaunawarsu da wakilan ASUU, ya ce ba dole ba ne ASUU ta dauki wata guda ta na yajin-aikin.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi yana ganin yajin-aikin na kungiyar malaman jami'a ya na daf da zuwa karshe idan abubuwa sun tafi yadda ake so.
Asali: Legit.ng