Da dumi-dumi: Rukunin farko na yan Najeriya mazauna Ukraine sun iso Abuja
- Rukunin farko na yan Najeriya mazauna Ukraine da suka yi kaura sakamakon yakin Rasha da Ukraine sun iso kasar
- Jirgin Max Air ne ya iso da su kasar a safiyar yau Juma'a, 4 ga watan Maris da misalin karfe 7:11
- A yanzu haka ana tsammanin saukan jirgi na gaba daga Hungary
Abuja - Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa rukunin farko na yan Najeriya da aka kwaso a yayin da ake tsaka da yakin Rasha da Ukraine sun iso babbar birnin tarayya, Abuja.
Sun isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 7:11 na safiyar yau Juma’a, 4 ga watan Maris, a jirgin Max Air, The Cable ta rahoto.
Jaridar The Nation ta kuma rahoto cewa gwamnatin tarayya za ta baiwa kowannen su dala 100.
Jaridar Independent ta rahoto cewa a yanzu haka ana tsammanin saukan jirgi na gaba daga Hungary.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Laraba ne gwamnatin taryya ta amince da dala miliyan 8.5 domin gaggauta kwaso yan Najeriya 5,000 da ke makale sakamakon yakin Rasha da Ukraine.
Da farko gwamnatin ta shirya dauko rukunin farko a ranar Alhamis, amma sai aka samu tsaiko. Don haka sai aka dage tashin jirgin.
Wadanda aka kwason sun samu tarba a Abuja daga Edward Adedokun, daraktan bincike da ceto na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA); jami’an hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), da kuma hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA).
Jimillar mutane 411 da aka kwashe tare da ma’aikatan ofishin jakadancin kasar ne suka iso Najeriya.
Dalilin da yasa aka jinkirta jigilar yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a Ukraine ranar Alhamis
A gefe guda, mun kawo a baya cewa dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta jinkirta jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine zuwa gida ranar Alhamis kamar yadda akayi alkawari ya bayyana.
Daily Trust ta ruwaito wani babban jami'in gwamnati da cewa wasu cikin wadanda ake kokarin jigila sun ki hawa jirgi saboda basu son dawowa Najeriya.
Tun lokacin da yakin ya barke, wasu sun gudu Romania, Hungary, Slovakia da Poland don neman mafaka.
Asali: Legit.ng