Tashin Hankali: An dasa Bam a wani gidan Kallon Kwallon Kafa a jihar Kaduna

Tashin Hankali: An dasa Bam a wani gidan Kallon Kwallon Kafa a jihar Kaduna

  • Mutane na tsaka da Kallo a wani gidan kallon kwallon kafa aka gano wani Bam da aka dasa a gidan dake Otal ɗin Larry Breeze Bar
  • Bayan samun rahoto, kwararrun jami'an yan sanda na sashin kwance abin fashewa suka dira wurin, kuma suka yi nasarar cire shi
  • A baya, gwamnatin Kaduna ta gargaɗi mazauna jihar su sanya ido kan abubuwan dake wakana a zagayen su, kuma su kai rahoto

Kaduna - Dakarun hukumar yan sanda sun gano wani Bam da aka dasa a gidan Kallo a Anguwar Romi dake karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna, kuma sun warware shi.

A rahoton Aminiya, Hukumar yan sanda ta bayyana cewa ta samu rahoton ganin wani abun fashewa a gidan Kallon Kwallon dake Hotel ɗin Larry Breeze Bar.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mutane sun gano Bam ɗin ne yayin da suke tsaka da Kallo.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Taswirar jihar Kaduna
Tashin Hankali: An dasa Bam a wani gidan Kallon Kwallon Kafa a jihar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A kalamansa, Kakakin yan sandan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan samun rahoton ne muka tura dakarun yan sanda na sashin kwararru a bangaren kwance ababen fashewa nan take, suka dira wurin kuma suka samu nasarar warware Bam ɗin."

Haka nan kuma, Jalige ya bukaci al'ummar jihar su sa ido kan abubuwan dake wakana a zagayensu, kuma su gaggauta kai rahoton abin da ba su amince da shi ba ga jami'an tsaro mafi kusa.

Kakakin yan sandan ya yi kira ga mutane su kwantar da hankulansu kuma su cigaba da harkokin su na yau da kullum ba tare da damuwa ba.

Wane mataki hukumomi ke ɗauka?

ASP Jalige yace hukumar yan sanda ta fara bincike kan bama-baman domin binciko waɗan da ke da hannu da dasa su.

Gano Bam ɗin ya zo ne bayan gwamnatin Kaduna ta fitar da sanarwar gargaɗin mutanen jihar kan shirin yan ta'adda na dasa bama-bamai a wuraren taruwar jama'a.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Gwamnatin ta yi wannan gargaɗin ne bayan fashewar wani Bam a Ginin wani tsohon Hotel dake Kabala, a Kaduna.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya

Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.

A halin yanzun dakarun sojoji sun bazama cikin daji domin nemo gawar mutumin, bayan sun yi gaba da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262